Rafin bakan gizo mai sihiri
Mimi Werna
Edwin Irabor

Yan'uwa uku Udoo, Erdoo da Eryum, suna sauraran yadda rowan sama ke sauti (da yake sauka), suna kuma son rawa a ciki, su kuma tava bakangizon da ya bayyana a sararin sama. Mama ta ce "A'a."

Suka yi kuka, da fatan zata canja ra'ayinta, amma hakan bai yi amfana ba. Har ma Eryum yayi qoqarin sulalewa ya fita gidan domin ya ga bakangizon.

1

Mama ta kama shi kafin ya fita. Tayi magana da murya mai ƙarfi saboda Eryum da 'yan'uwan sa mata suma su ji.

"Zaku iya kama mura," ta ce. "Gashi baku son ferfesu kuma dole ne ku sha in har mura ta kamaku," ta yi murmushi.

2

Da fatan za su ce ta ba su tatsuniya, sai ta ce, "Bakangizo, rafi ne mai sihiri da ke da ikon warkarwa," amma yana can cikin sararin sama yadda baza ku iya taɓawa ba. Idan mura ta kamaku, bakangizo ba zai iya taimakon ku ba.

Yaran suka yi tunanin wannan maganar.

3

"Mama don Allah ki ba mu tatsuniyar mu ta bakangizo," Erdoo ta ce. "I, don Allah mama ni ma ina so in ji," Udoo ma ta sa baki. "Nima haka," Eryum ya roƙa, tare da ɗaga ƙananan yatsu uku sama.

Da wasa ta ce, "Bari mu gani mmmmm! Toh, ku matso kusa, ga mama mai ba da tatsuniya nan!"

4

Erdoo ta ruga da gudu ta ɗauko muciyan da suke amfani da ita mai nuna alamar izini. Da ta ɗauko, sai ta miƙawa Mama. Sai Eryum ya ɗauko ɗankwalin da Mama za ta ɗaura. Wannan bai taɓa fasa bata sifan mai tastuniya ba.

Sai suka zauna shuru don suji wannan tastuniyar da suka riga suka ji saudayawa. Udoo ta hura usir mai cewa Mama ta fara, sai tastuniya ta soma.

5

"Da can, bakangizo rafi ne mai sihiri. An ɓoye shi ne cikin dazuzzuka mai launin kore a garin Mbadede. Saboda yana da ikon warkarwa saboda, ana tsaron rafin."

Idan kuna ciwo, sai ku sha ruwan. Bakagizon na farin ciki a kullum ya raba ruwan da masu buƙata. Amma fa, ba ya son mutane mara sa kirki.

6

"Saboda sihirin rafin, ana samun madara mai sanyi a bakin rafin. Duk wanda ya zo shan ruwan rafin, ya kan more wannan madara mai sanyi ɗin, musamman ma yara.

Wannan madara mai sanyi ɗin daga rafin na da launuka kamar ja, ruwan lemo, ruwan ɗoruwa, kore, shudi, lilak, da ruwa mai haɗin shuɗi."

7

"Wata rana, wata gagararriyar tsohuwa mai suna Mbom tazo daga wata ƙasa mai nisa. Da shigar ta garin, sai ta haɗu da wani maitsaro. Bai san ta ba kuma sai ya ji wani iri a jikin sa game da tsohuwar. Amma bai mai da hankali ga yanayin da ya ji game da ita ba.

Sai ya nuna mata hanyar zuwa rafin sannan yace da ita ta girmama rafin. Mbom ta amince sai ta wuce zuwa rafin."

8

"Da ta sha ruwan, sai ta warke. Sai ta waiwaya ta tabbatar babu mai ganin ta.

Mbom ta ɗauki dutse ta jefa cikin rafin. Sai ta ga yadda ruwan ya yi sama ya kuma warwatsu yana bi koina. Sai ta ji daɗi, ta ɗauki sandan itace ta jefa ciki, ruwan ya sake yin yadda yayi da farko."

9

"Mbom ta yi tsalle ta faɗa cikin rafin da fatan ta sami rai dawwamamme. Tana faɗawa cikin rafin, sai ruwan ya taso sama. Ya cigaba da hawa can sama yadda ba zai sake dawowa garin Mbadede ba. Amma, wasu lokuta, bakangizon na bayyana ne bayan ruwan sama domin ya sake ji kamar rafi.

"Kurungus. Karshen tatsuniya ta ke nan," Mama ta ce.

10

"Toh kaunatattuna, ku faɗa min dalilin da yasa kuke son wannan tatsuniyar sosai? Mama ta tambaya. "Sau da dama kukan ce in baku wannan tatsuniyar."

"Ina son ta ne saboda tana tuna min da in yi la'akari da yadda nake ji game da mutane," Udoo ta ce tana murmushi.

"Tana tuna min da launukan da bakangizo ke da shi." Erdoo ta kara.

11

Eryum ma yayi ƙoƙarin faɗin nasa ra'ayin da fatan zai yi dace, "Ina son tatsuniyar ne domin tana tuna min da madara mai sanyi! Za'a iya bani yanzu, don Allah?"

"Mmmmm. Akwai sanyi yanzu, bari mu sha madara mai sanyi gobe ko?" Mama ta ce. "Sai ta sake cewa wata rana, zan baku tatsuniyar yadda ƙarshen Bakangizo ta kasance."

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Rafin bakan gizo mai sihiri
Author - Mimi Werna
Translation - Kabuk Salomi
Illustration - Edwin Irabor
Language - Hausa (Nigeria)
Level - Read aloud