Kande Sarkin Surutu
Gaspah Juma
Jesse Breytenbach

A wani lokaci mai tsawo, an yi wata yarinya mai suna Kande. Kande yarinya ce mai surutun tsiya. Duk da cewa mahaifiyarta tana kwaɓarta a kan hakan, amma Kande ta yi kunnen uwar shegu.

1

Gwaggon Kande tana zaune ne a wani kwari kusa da ƙauyen su Kande. Wata rana sai ta faɗi rashin lafiya kuma babu mai jinyarta.

2

Mahaifiyar Kande ta yi dare wurin abinci, sai ta kira Kande ta ba ta kai wa Goggonta.

3

Tana cikin tafiya, sai ta ci karo da Shanshani, ba ta san Kura ce ta rikiɗe ba.

4

Sai Shanshani ya ce ma ta, "Me ne ne a cikin wannan akushin?" Sai Kande ta ka da baki ta ce, "Nama ne da ƙwai da madara."

5

Kande ta ci gaba da cewa, "Zan kai wa Gwaggona wannan abincin ne, saboda ba ta da lafiya." Sai Shanshani ya fara tanɗar baki yana lashe-lashe saboda ƙanshi naman dake cikin akushin Kande.

6

Saboda haka, sai Shanshani ya ruga a guje ya shiga gidan Gwaggon Kande.

7

Yana zuwa ya haɗiye ta, kuma ya ɗauki bargonta ya kwanta ya lulluɓa.

8

Da Kande ta iso sai ta ji gidan ya yi tsit, sai ta fara kira "Gwaggo, Gwaggo, kina ina?"

9

Kande ba ta ji muryar Gwaggonta ba. Sai ta shiga ɗakin da take kwance, cikin mamaki sai ta ga mutum a kwance ya lulluɓa da ƙaton bargo.

10

Kande ta ce, "Gwaggo ya ya kunnuwanki yau suka ƙara girma?"

Shanshani ya amsa daga cikin bargo, "Domin inji ki sosai."

11

Kande ta sake cewa, "Gwaggo ya ya na ga idanun ki sun yi girma yau?

Shanshani ya amsa daga cikin bargo, "Domin in gan ki sosai."

12

Kande a ƙarshe ta ce, "Gwaggo, ya ya yau na ga bakinki ya zama ƙato?"

Shanshani ya amsa, "Don na cinye ki." Sai ya yi tsalle daga cikin bargon ya haɗiye Kande.

13

Kande ta ci gaba da surutu a cikin Shanshani kuma tana yin tambayoyi iri-iri.

14

A qarshe, Shanshani ya gaji da surutun Kande da tambayoyinta sai ya amayar da ita da Gwaggonta.

15

Mutanen ƙauyen suka rugo, kuma suka kuɓutar da Kande da Gwggonta.

Tun daga wannan ranar, Kande ta daina surutu a wurin mutanen da ba ta sani ba.

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Kande Sarkin Surutu
Author - Gaspah Juma
Translation - Binta Usaini Umar, Jamilah Abba
Illustration - Jesse Breytenbach
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs