Tseren haɗin kan Afirika
Ursula Nafula
Brian Wambi

Mudi da Tanko abokan juna ne masu sha'awar guje-guje. Kullum suna guje-guje tare.

1

Wata rana, Tanko yace, ''Bari mu yi tsere a cikin Nahiyarmu. Bari muyi tsere domin goyon bayan haɗin kan Afirika!" "Mu tafi!" Mudi ya amsa.

2

Sun yanke shawarar ɗaukar fitilar haɗin kai a tafiyarsu. Sun fara tseren daga Kudu, a birnin Kef.

3

Daga Afirika ta Kudu sun bi ta gaɓar kogi ta yamma. Sun bi ta Kasashen Namibiya, Angola, Haɗaɗɗiyar Daular Kongo, Kongo da Kamaru. Sun huta a Abuja.

4

'Yan tseren Afirika ta yamma sun haɗu da abokansu na Nijeriya. Sun ci gaba tare, ta bin kogin Neja zuwa yamma.

5

Yanayin yashin ƙasar Mali ya basu wahalar ci gaba da tseren. Mudi shi ne gwarzo daga cikin su. Ya jagoran ce su cikin nasara.

6

A kogin Gini da ke Kwanakiri 'yan tseren suka wanke ƙurar da suka kwaso. Sai suka yanke shawarar tsere ta Maroko da Senegal da Mauritaniya.

7

A garin Kasabalanka 'yan tseren sun yi wasa da wasu matasa a gaɓar kogi. Daga nan, suka ci gaba zuwa tsallaken Afirika ta Arewa.

8

Tseren ya shiga ƙasashen Aljeriya da Libiya, sannan su ka tsaya a ƙasar Misira don ziyartar dala. Daga nan suka yi gaba zuwa gabas ta bin tekun Nilu zuwa Yuganda.

9

Sun ci gaba da tsere ta cikin Sahara da gandun dazuzzuka daban daban. An samu Karin matasa a garin Kampala. Gungun 'yan tseren sun nufi gaɓar kogin Kenya.

10

A garin Mumbasa sun zauna a gaɓar kogin
inda suka ci shinkafa da Kwakwa da Kifi.
Tanko ya ce, "Ku zo mu dauki fitilar haɗin kan Afirirka zuwa tsaunin Kilimanjaru."

11

Amma Tanko ya gaji. A kan hanya zuwa Tanzaniya, ya faɗi kasa. Gaba ɗaya 'yan tseren suka dakata kuma suka juya baya domin taimakawa Tanko.

12

Tanko ya miƙawa Mudi fitila. Ya ce, "Ka tafi da fitilar zuwa tsaunin Kilimanjaru. Ka kunna ta don haɗa kan Afirika."

13

Jama'a sun yi wa 'yan tseren tafi, "Ku gwaraza ne." Bayan haska fitilar haɗin kai a Kilimanjaro, sai suka juyo zuwa Afirika ta Kudu.

14

Sun dakata domin yin ninƙaya a tafkin Malawi. Mudi ya ce wa Tanko, "Munyi tsere tun daga Kudu zuwa Arewa sannan muka sake dawowa. Yanzu tafiyar mu ta ƙare."

15

A ƙarshe masu tseren haɗin kai sun dauki fitilar zuwa Kasar Zinbabuwe. 'Yan kallon sun taru a wannan muhimmin wuri. "Tanko yayi murmushi, ya ce tsere ke nan!"

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Tseren haɗin kan Afirika
Author - Ursula Nafula, Nina Orange
Translation - Hamza Usman Shehu, Muhammad Tijjani Ibrahim
Illustration - Brian Wambi
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences