Abotar Ɗan Taure da Ɗan Damisa
Belainesh Woubishet
Jesse Pietersen

Wata rana ɗan taure da ɗan damisa suka ƙulla abota.

1

Ana nan, sai suka tafi daji don su yi wasa.

2

Ɗan taure da ɗan damisa suka yi dare sosai kafin su dawo gida.

3

Sai ɗan taure ya ce wa innarsa, "Yau na haɗu da wani aboki mai kirki. Gobe ma za mu sake haɗuwa da shi."

4

Sai innarsa ta ce, "Wannan ba abokinka ba ne, yau ma na gode wa Allah da ka dawo lafiya." Don haka, kada ka je wurinsa gobe.

5

Shi ma ɗan damisa ya faɗa wa innarsa cewa, "Na haɗu da wani aboki mai kirki. Gobe ma zamu sake haɗuwa da shi."

6

Damisa ta cika da mamaki. sannan ta ce, "Dana, me ya sa ba ka cinye shi ba? idan kun haɗu gobe kar ka dawo gida sai ka cinye shi."

7

Washegari, sai ɗan damisa ya tafi ƙauyensu ɗan taure yana nemansa wurjanjan.

8

Amma ɗan taure ya laɓe a bayan innarsa. Ya ƙi fitowa daga gida.

9

Ɗan damisa ya taƙarƙare yana cewa, "Abokina, abokina fito mana mu yi wasa!"

10

Ɗan taure ya numfasa ya leƙo, sannan ya ce, "Innata ta faɗa min kai ba abokina ba ne, hanyar jirgi daban da ta mota," ni kuma ina jin maganar innata.

11

Don haka, jikin ɗan damisa ya yi sanyi, ya juya gida cike da takaici.

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Abotar Ɗan Taure da Ɗan Damisa
Author - Belainesh Woubishet
Translation - Binta Usaini Umar, Jamilah Abba
Illustration - Jesse Pietersen
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences