Yadda Kunkuru Ya Samu Karkataccen Hanci
Taiwo Ẹhinẹni
Marlene Visser

Kunkuru da Kurege suna buƙatar kuɗi.

1

Suka yi farantai na sayarwa, suka kai kasuwa.

2

Kunkuru yaga ana faɗa a kasuwa.

3

Kurege da Jaɓa suna faɗa.

4

"Ki rabu da abokina!" Kunkuru yayi tsawa.

5

Sai Jaɓa ta ciji Kunkuru a hanci.

6

Sai fasashen hancinsa ya fara ciwo.

7

Kunkuru ya samu karkataccen hanci saboda gaggawar shiga faɗa.

8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Yadda Kunkuru Ya Samu Karkataccen Hanci
Author - Taiwo Ẹhinẹni
Translation - Aysha I. Sada
Illustration - Marlene Visser
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First words