Birai a Lokacin Fari
Alice Edui

Damina ba ta sauka ba, saboda haka ƙasa ta bushe.

1

Wannan biranyar ta bar gida don neman ruwa da abinci.

2

Tana kai-kawo cikin tudu da kwari.

3

Sai ta iso wani wuri da ake kira Tirkol.

4

Biranyar ta yi farin cikin isa wannan wurin.

5

Ta ci 'ya'yan itace ta yi ɓulɓul. Sai dai, ta yi kewar ƙawayenta.

6

Don haka, biranyar ta kama hanyar gida.

7

Sauran biran suka cika da farin cikin ganinta.

8

Suka tambaye ta, "A ina wannan ƙasaitaccen wuri mai 'ya'yan itatuwa yake?"

9

"Zan kai ku wajen," cewar biranyar.

10

Sauran biran suna ƙaunar Tirkol. Sai suka ƙuduri zamansu a nan har abada.

11

Amma biran Tirkol sai suka damu.

12

Suka ce, "Waɗannan baƙin biran za su cinye mana duk abincinmu."

13

Don haka, biran Tirkol sai suka kai wa baƙin birannan farmaki.

14

"Me zai sa mu yi fada?" Wani a cikinsu ya ce, bayan akwai abinci mai yawa.

15

Wannan haka ne. Sai suka ƙudurta su zauna tare cikin lumana.

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Birai a Lokacin Fari
Author - Alice Edui
Translation - Shamsuddeen Abdulkadir Dallaje
Illustration - , Salim Kasamba
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First words