Wani Dogon Mutum
Cornelius Wambi Gulere
Catherine Groenewald

Fartanyar sa yar ƙarama ce.

1

Ƙofar ɗakinsa ma 'yar gajera ce.

2

Gadon barcinsa ma gajere ne.

3

Kekensa ma ɗan gajere ne.

4

Kai, wannan mutum dogo ne qwarai!

5

Ya maida ƙotar fartanyarsa mai tsawo sosai.

6

Kyaurayen ƙofofin ɗakinsa ma ya sanya masu tsayi sosai'

7

Ya maida gadon barcinsa mai tsayi sosai.

8

Ya sayo keke mai tsawo sosai.

9

Ya kan zauna a doguwar kujera. Ya ci abinci da dogon cokali mai yatsu.

10

A ƙarshe ya bar gidansa, ya koma dokar daji. Ya rayu shekaru masu yawa.

11
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Wani Dogon Mutum
Author - Cornelius Wambi Gulere
Translation - Muhammad Tukur Bala
Illustration - Catherine Groenewald
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First words