Zomo Ya Yi Wa Kunkuru Wayo
Maimouna Jallow
Catherine Groenewald

Gata nan gata nanku. wani Kunkuru ne mai aiki tuƙuru, ya daɗe yana tattalin 'yan kuɗinsa.

1

Bayan ya ajiye aiki, sai ya ga yana da makudan kudi.

2

Don haka sai ya yanke shawarar sayen babbar gona, ya riƙa nomawa.

3

Labarin kunkuru na neman gona ya saya, ya cika karkarar.

4

Zomo na jin labarin kunkuru na son sayen gona, sai ya tafi wajen kunkurun ya ce zai taimaka masa.

5

Sai ya kai kunkuru wata makekiyar gona ya nuna masa da cewa tasa ce.

6

Kunkuru ya ga gona ta yi masa, don haka aka yi ciniki tsakaninsa da Zomo, ya kuma biya.

7

Gari na wayewa sai kunkuru ya gayyaci abokansa don a fara shuka a gonar.

8

Isar su ke da wuya sai suka iske ruwa ya shafe filin. Sai abokan suka tuntsire da dariya suna ce masa,ina filin naka?

9

Ganin haka sai Kunkuru ya fahimci zomo ya cuce shi, ashe ya sayar masa da gaɓar kogi ne ba filin gona ba.

10

Tashin kunkure ke da wuya, sai ya wuce wurin alƙali, wato giwa ya kai ƙara. Da jin koken kunkuru, sai ta umurci zaki da ya kamo zomo.

11

Zomo na jin zaki ya dumfaro gidansa, sai ya fito ya tarbi zakin da murna yana cewa, sauri nake yi don zan je mu kori kerkecinn da suka shigo gari.

12

Sai zomo ya bi gari yana kuka irin na kerkeci, don haka zaki ya tsorata ya ruga a guje.

13

Daga nan sai zomo ya yi gaba da kuɗin Kunkuru. Shi kuwa kunkuru 'yan uwa da abokan arziki suka taimaka masa da wata gonar.

14
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Zomo Ya Yi Wa Kunkuru Wayo
Author - Maimouna Jallow, Haji Gora Haji
Translation - Mukhtar Aliyu
Illustration - Catherine Groenewald, Katrin Coetzer, Padmanabha, Wiehan de Jager
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences