Saniya mai ƙaho Ɗaya
Sebongile Daniel
Marion Drew

Kai! Akwai saniya mai kyau a gidan mu.

1

Ta na da ƙaho daya kuma ba ta da jela.

2

Ta na da ƙiba da ƙaton ciki.

3

Saniyar tana da ƙarfi sosai.

4

Makiyayinmu na son wannan saniya matuƙa.

5

Yayin da sauran shanu ke yin kiwo tare, ita ta kan yi kiwo a ware.

6

Wannan Saniya mafaɗaciya ce, don haka sauran shanu suke ƙaurace mata.

7

Idan ka haɗu da irin wannan saniyar, yaya za ka yi?

8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Saniya mai ƙaho Ɗaya
Author - Sebongile Daniel, Mpho Ntlhanngoe, Khothatso Ranoosi
Translation - Muhammad Umar, Rabiu Abdullahi, Sa'adatu Sani Hanga
Illustration - Marion Drew
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First words