Anansi Raggo
Ghanaian folktale
Wiehan de Jager

Anansi Gizo ne raggo.

1

Yana son abinci, amma raggwancinsa kan hana shi girki.

2

Anansi ya ziyarci zomo, ya ce, "In zo muci kayan lambu?"

3

Zomo ya ce, "Eh! sai dai ka taya ni juya miyar." Amma Anansi raggo ne.

4

Anansi ya ce, "Bari in dawo."

5

Anansi ya saka yana a ƙafarsa da jikin tukunyar zomo.

6

"Ka ja yanar idan kayan lambun sun nuna," inji Anansi.

7

Ya ƙara gaba, "Birai, in zo mu ci wakenku?" "Eh! Ka taya mu dafawa "

8

"Zan dawo," inji Anansi. Ya kuma sake saka yana.

9

"Gwanki, in zo muci dankalinka?" "Eh! Taimaka mini mu shirya abinci."

10

"Zan dawo," inji Anansi. Ya kuma sake saka yana.

11

Jim kaɗan, kowace ƙafa daga ƙafafuwan Anansi 8 an ɗaure ta a jikin tukunya.

12

Anansi yaji anja ƙafarsa ta 2, Sannan ta 3.

13

Duka ƙafafuwan 8 a ka dinga jan su! "Ku bar ja!" Anansi ya fasa kuka.

14

Ba wanda yaji kukan Anansi.

15

Ƙafafun Anansi suka miƙe! Wannan ya sa ƙafar Gizo ta zama siririya.

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Anansi Raggo
Author - Ghanaian folktale
Translation - Habibu Ahmed Jibrin, Sani Masama Garba
Illustration - Wiehan de Jager
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences