Tabarmar Ta Masumman Ta Binta
Ursula Nafula
Catherine Groenewald

Lokacin da Binta take yarinya, mahaifiyarta na shimfiɗe ta saman wata kyakkyawar tabarma.

Tantin Binta ta saƙa wannan tabarmar ta masumman da kaba.

1

Launin tabarmar ya fito sosai: Bula, ruwa hoda, tsanwa.

Ba tabarma ba ce kamar kowace tabarma da ke cikin ɗakinsu.

2

Ƙasar kewayen gidan a bushe take, ga zafi ga kuma duwatsu.

Ana ganin kunamu da micizai wani lokaci. Binta tana kiyaye ma wannan ƙwarirrika.

3

Mahaifiyarta tana cewa: "Wannan tabarmar tana kare ki da miyagun abubuwa."

4

Binta yarinya ce mai ilimi. Ta san inda rijiya ma fi kusa take.

5

Kuma ta san inda garin kakarta yake. Takan je wani lokaci don ta sha nonon taguwa.

6

Wata rana, ba ta yi sa'a. Sai ta tafi garin kakarta, bisan hanya sai ta ɓace cikin duwatsu. Tsoro ya kama ta.

7

Wata rana, ba ta yi sa'a ba. Sai ta tafi garin kakarta, bisan hanya sai ta ɓace cikin duwatsu. Tsoro ya kama ta.

8

Ga mafarkin da ta yi: Ta kwance saman tabarmarta. Kakarta ta miƙa mata nonon taguwa cikin wani kopi. Lokacin da ta miƙo hannu ta amsa sai ta farka.

9

Binta ta buɗe idonta a hankali. Lokacin da ta ɗaga kai, sai ta ga wani tsuntsu bula saman wani reshe.

10

Da Binta ta tashi, tsuntsu ya hira ya gwada mata hanya. Binta ta bi tsuntsun.

11

Binta ta zo wani wuri inda hanya ta rabu biyu (2). Tsuntsun ya yadda wani guntun tabarma mai kama da tabarmar Binta.

12

Da ta ɗauki guntun tabarmar, Binta ta ga shaidar sawu mahaifiyarta. Can gaba kuma sai ta ga rijiyar da suke janyo ruwa.

13

Ƴan uwanta suna waƙa, suna rawa don sun tarbe ta. Sun yanka akuya, sun gasa don murnar ganin Binta ta komo.

14

Binta ta zamna saman tabarmarta kuma ta fara cin naman da aka gasa mata.

15
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Tabarmar Ta Masumman Ta Binta
Author - Ursula Nafula
Adaptation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Catherine Groenewald
Language - Hausa (Niger)
Level - First paragraphs