Hadiza Da Kuraye
Sarah Nangobi
Wiehan de Jager

A lokacin da, an yi wata yarinya mai sunan Hadiza, ta na rayuwa ne tare da uwayenta da suke kusa da garin budongo. Wata rana, uwar Hadiza ta aike ta rijiya ɗibar ruwa.

1

Bisan hanyarta, ta gamu da abokananta. Za su tafiya cikin daji neman itace. Hadiza tana son ta bi su. "Don Allah ku jirayeni ƙarƙashin iccen kuka!" in ji ta. "Za ni tafiya in ɗebo ma uwata ruwa." Amma abokananta ba su son su jiraye ta.

2

"Da kyau, za ni cimmaku cikin daji" in ji Hadiza. Ta je da gudu ta ɗebo ruwan, ta kawo ma uwarta. Kuma ta je cikin dajin ta tararda abokananta.

3

Ta bi ta hanyar da za ta kai ta wajen wani marmaro. Daga wata gaɓar ruwan, akwai ƙananan hanyoyi da suke kai ka ko'ina. "Ta ina suka bi?" tana tambayar kanta.

4

Ta ɗauki hanyar da ta fi nisa, take tafiya, take tafiya, amman ba ta cimma bokananta ba. Ta gaji ƙwarai sai ta zamna ƙarƙashin wata bushiya don ta futa, daga nan kwana ya ɗauke ta.

5

Lokacin da Hadiza ta farka, dare ya yi. Cikin dufu, sai ta hango wasu idanu masarori suna walƙiya. Kuraye sun kewaye ta! Ta firgita sosai har ba ta iya kuwa. Ta so ta tsere amma kurayen da suka kewayeta suma yunwa suke ji.

6

"Kar da kimotsa" inji babban kuren, da wata ƙwararar murya. "Idan kin yi gudu, za mu cinye ki." Sai ta roƙe su, "don Allah, ku bar ni in tafi gidanmu!"

7

Amma maimakon haka, sai kurayen suka kai ta gidansu can cikin daji. Wani ɗaki ne mai dauɗa, cike da ƙasusuwa sai ƙuda suna ta yin bobowa. Ta yi kwance kamar ta yi barci.

8

Cikin dufu, ta ji kurayen suna yin shawara. "Yaya wutar?" wata kura ta tambaya. "Ko ruwan sun tafasa?" "Komi ya kammalu" aka bata amsa. "In janyo ta?" "e, e!" sauran kurayen suna gurnani. "Yunwa muke ji!" Sun shirya su fito da Hadiza daga cikin ɗakin.

9

Sai babban kuren ya ce, "Kai kuraye, ku dakata. Kar kumanta ƙa'idar wannan garin. Babu kuren da za ya ci shi kaɗai. Ya kamata mu gayyaci duk iyalenmu don mu ci abincin." "Za ni gayyaci sirikaina" in ji matarshi. "Za ni je in kiranyo ƴan uwana" in ji ƙaramar kurar. "Ni ko za ni tsayawa don in fake abincinmu" in ji babban kuren.

10

Babban kure ya zauna bakin ƙofar ɗakin, sauran ko suka barbazu cikin daji. Can da jimawa, babban kure ya fara angaje gaban wutar da suka kunna. Nan take har ya fara shinkori. Sa'ar Hadiza ke nan! Amma, yaya za ta bi kusan da kuren? Saboda girmanshi ya tare ƙofar fita.

11

Hanya guda ce, ta tsalaka sama, ta faɗa wancen ɓangaren na kuren, sai ta zuba da gudu bakin ƙoƙarinta.

12

Ko da sauran kurayen suka dawo, suka lura da abun da ya faru, suka je neman Hadiza, cikin baƙin-ciki da takaici. Amma, ina, ta yi nisa.

13

Da ta iso cikin garinsu, wani mutum ya gane ta sai ya sa kuwa, "Hadiza, Hadiza ta dawo, Hadiza ta dawo" Babanta da uwarta suka tarbe ta da gudu, suka rungume ta, su na yi wa Allah godiya da ya ceci diyarsu, "Hadiza, Hadiza, mun aza kin mutu!"

14

Tun daga wanna ranar, Hadiza da sauran yaran, basu sake komawa cikin daji su kaɗai.

15
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Hadiza Da Kuraye
Author - Sarah Nangobi
Adaptation - Plan Niger - Projet NECS - Usaid
Illustration - Wiehan de Jager
Language - Hausa (Niger)
Level - Longer paragraphs