

Wani lokaci, Dan Akuya shi ne sarkin dabbobi da tsuntaye.
Sai ya kirawo su taro.
Dan Akuya ya ce musu ya yi mafarki.
Duk sai suka saurara.
Ya yi mafarki a kan yunwa.
"Yaya za mu yi to?" Muzuru ta tambaya.
Kaza da Agwagwa suka ce, "Sai mu tara abinci a cikin rumbun sarki."
Sarki Dan Akuya ya ce, "A kama duk wani wanda ya ki bin doka a daure shi."
Da lokacin zaben sabon sarki ya zagayo.
Sai suka zabi Muzuru.
Amma Dan Akuya ba ya son Muzuru ya zama sarki.
"Ni ne nan sarkin ku," Dan Akuya ya fada cikin fushi.
Dan Akuya bai dauki abinci ya kaiwa sarki ba.
Sai Saniya ta ce, "To yanzu ya zamu yi?"
Sai dabbobi da tsuntsaye su ka tattauna.
Sun yi fishi da Dan Akuya.
Sai Kare ya ce, "Koyaushe ina tare da shi lokacin da yake sarki."
Sai Tinkiya ta ce, "Ni nake saka wa 'ya'yansa kaya lokacin da yake sarki."
Alade kuwa ya koka da cewa, "Ni ne nake kula da gonarsa lokacin da yake sarki."
"Shin dan Akuya yana zaton zai ta zama a sarki ne har abada?" Tinkiya ta tambaya.
Dukkan dabbobi suka amince cewa dan akuya dole ne ya kaiwa sabon sarki abinci.
Sai suka je suka same shi yana hutawa.
Dan Akuya ya ce, "Har abada ni zan cigaba da zama sarki."
"Za mu daure ka da igiya, sannan mu kai ka gaban sabon sarki."
Saniya ta jawo Dan Akuya zuwa fadar sarki.
Sauran dabbobi su kai shewa.
Shi ya sa har yanzu Dan Akuya ba ya yin tafiya idan ana jan shi.

