Muguwar Shawara
Magabi Eynew Gessesse
Brian Wambi

Kombe da Juma sun kasance makota talakawa.

Suna yin komai a tare da kansu.

1

Sai suka yi tunanin su sayi jaki.

Domin ya dinga daukar musu kaya.

2

Kombe ya kawo shawara, "Mu hada kudi mu sayi jaki."

Suka yi farin ciki.

3

Ana haka, sai baban Kombe ya mutu. Kombe ya samu dukiya mai yawa.

Nan da nan sai ya manta da abokinsa Juma.

4

Kombe yana son ya yanka jakinsu, ya ba karnukansa nama.

Juma yana bukatar jakin wajen yin aiki.

5

Sai suka je wajen Alkali. Shi kuma ya ce, "Sai s raba jakin gida biyu, kowannenku ya dauki rabi."

6

Sai Kombe ya kashe jakin.

Juma ya koma daukar kaya da kansa.

7

Daga nan sai Kombe ya fara tunanin kona bukkarsa, ya gina sabuwa.

8

Juma ya ce, "Nima tawa za ta kone, idan ka kona taka."

Amma sai alkali ya sake ba Kombe nasara.

9

Bukkar Juma ta kone kurmus.

Alkali kuwa ya ce, "Ai Kombe iya bukkarsa kawai ya kona."

10

Juma ya dawo ba shi da gida kuma ba shi da jaki, dan haka yake kwana karkashin bishiya shi da iyalansa.

11

Juma ya yi aiki sosai a gona.

Shukar wakensa ta yi kyau matuka.

12

Sai yaran Kombe suka je suka ci wake mai yawa a gonar Juma.

13

Yaran suka ce da Juma, "Ka je ka tambayi babanmu domin ya biya ka kudin wakenka."

14

Juma ya je wajen Kombe, ya ce masa, "Ni bana son kudinka, wakena kawai nake so."

15

Sai alkali ya ce da juma, "Ka je ka yanka yaran sannan ka debi wakenka."

16

Juma ya ki sauraron Kombe.

Kombe ya dinga rokonsa, "Ka bari manya su shiga maganar."

17

Sai dattawan suka ce da Kombe, "Ka kashe masa jakinsa. Kuma ka kona bukkarsa."

18

Sai suka ce da Juma, "Kai kuma kashe yaran kombe ba abu ne mai kyau ba."

19

Kombe ya bawa Juma rabin dukiyarsa.

Daga nan suka zauna cikin farinciki.

20
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Muguwar Shawara
Author - Magabi Eynew Gessesse, Elizabeth Laird
Translation - Aisha Umar Abdullahi
Illustration - Brian Wambi
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences