

Watarana Zomo yana cikin tafiya a gefen kogi.
Ita ma Dorina ta fito shakatawa, kuma ta ci korayen ciyayi.
Dorina ba ta san cewa Zomo na wajen ba, sai ta taka masa kafa.
Zomo ya ji zafi ya fara ihu yana cewa, "Ke Dorina ba ki ga kin taka min kafa ba?"
Sai Dorina ta ba Zomo hakuri ta ce, "Ayya, yi hakuri Zomo, ban gan ka ba ne, ka yafe min."
Amma Zomo bai yarda ba, sai ya cigaba da ihu yana cewa, "Ba wani nan, kina sane kika taka ni, kuma za ki gani, watarana sai na rama!"
Daga nan sai Zomo ya tafi wajen Wuta ya ce, "Je ki kona Dorina idan ta fito daga cikin kogi za ta ci ciyawa, domin ta taka ni!"
Sai Wuta ta ce, "Ba damuwa abokina. Zan yi duk yadda ka ce."
Jimawa kadan, Dorina ta fito tana cin ciyawa a nesa da kogi, kwatsam! Sai Wuta ta tashi. Fara yaduwa.
Ta fara kona gashin Dorina.
Dorina ta fara kuka, ta ruga a guje ta fada cikin ruwa. Duka gashinta wuta ta kone shi.
Dorina ta cigaba da kuka tana cewa, "Wayyo gashina, gashina ya kone a cikin wuta, shikenan yanzu bani da gashi, wayyo kyakkyawan gashina!"
Zomo ya yi farinciki cewa gashin Dorina ya kone.
Tun daga wannan ranar, Dorina ba ta nisa daga bakin kogi sabo da tsoron wuta.

