

A wata shekara lokacin bazara ya yi tsaho sosai. Dan haka dukkan koguna suka kafe, sai kogin baiwa ne kadai bai kafe ba.
Dukkan dabbobi suna matukar jin kishirwa, dan haka suka kira taro a tsakaninsu.
Rakumi shi ne ya fara magana ya ce, "To kun san dai cewa dukkaninmu muna matukar jin kishirwa, sannan kuma dukkan koguna sun kafe, sai dai Kogin Baiwa shi kuma yana da nisa sosai. Yanzu ya ya za mu yi?"
Sai doki ya ba da shawara cewa, "Wasu daga cikinmu mu tafi Kogin Baiwa, mu sha ruwa sannan mu debo mu kawo wa sauran su sha."
Saniya ta ce, "Gaskiya wajen da nisa sosai, idan muka
tafi wadanda muka bari za su mutu kafin mu dawo."
Sai Tinkiya ta ce, "Maaa Maaa! Ni dai zan je Kogin Baiwa na sha ruwa."
Sai Akuya ma ta ce, "Meee Meee! Nima zan je Kogin Baiwa."
Sai Kaza ta ce, "Keee keee keee! Nima dai zan je Kogin Baiwa."
Dukkan dabbobin suna so su je, dan haka Rakumi ya jagorance su suka kama hanya.
Wannan tafiya ba mai sauki ba ce, Zabo shi ne a can baya. "Abokaina ni fa na gaji da tafiya, ba zan iya zuwa Kogin Baiwa ba," Zabo ya ce.
Sai Kaza ta hadiye Zabo.
Suka ci gaba da tafiya. Sai Kaza ta ce, "Gaskiya na gaji, na hakura ba na so na je Kogin Baiwa."
Sai Tinkiya ta hadiye Kaza.
Suna cikin tafiya sai Tinkiya ita ma ta gaji.
Sai ta ce, "Nima na gaji ba na bukatar zuwa Kogin Baiwa sam."
Sai Akuya ta hadiye Tinkiya.
A na cikin tafiya, Akuya ita ma ta gaza, domin ba za ta iy cigaba da tafiyar ba. Sai Doki ya juya ya hadiye Akuya.
Lokacin da Doki ya gaji da tafiya, sai Saniya ta juya ta hadiye shi.
Da Saniya ta gaza, sai Rakumi ya juya ya hadiye ta.
Da Rakumi ya ga shi kadai ya rage, sai ya yi iya kokarinsa domin ya isa Kogin Baiwa.
A karshe Rakumi ya isa Kogin Baiwa a gajiye bayan ya sha wahala.
Daga zuwa sai Rakumi ya kwanta ya amayo Saniya.
Ita kuma Saniya ta amayo Doki, shi kuma Doki ya amayo Akuya.
Ita kuma Akuya ta amayo Tinkiya, ita kuma Tinkiya ta amayo Kaza, ita kuma Kaza ta amayo Zabo.
Ta haka dukkan dabbobin suka samu dama suka sha ruwa a Kogin Baiwa.

