Alake mai son baki
Rasheedat Sadiq
African Storybook

Kwan, kwan!

Ana buga kofa!

1

Alake ta cika da farin ciki.

"Waye?" ta tambaya.

"Mummy mun yi baki!"

2

"To, ina zuwa," in ji maman Alake. "Ina jin matar Malam Hassan ce, ki bude mata kofa."

3

Alake ta bude kofar tana murmushi. "Sannu da zuwa Mama, ki shigo ciki, mamana tana zuwa ba da jimawa ba."

Matar Malam Hassan ta godewa Alake.

4

"In kawo miki abin sha?" Alake ta tambayeta.

"A a, ki barshi, bana jin kishirwa, na gode," in ji matar Malam Hassan.

5

"Sannu da zuwa matar Malam Hassan, yi hakuri na bar ki kina jira."

"Babu komai kawata, Alake ta ba ni kulawa."

6

Maman Alake ta yi murmushi.

Ta ce, "Ai Alake ta iya kula da baki sosai, ina alfahari da ita."

7

Alake ta iya kula da baki sosai!

8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Alake mai son baki
Author - Rasheedat Sadiq
Translation - Fatima Y Muhammad
Illustration - African Storybook, Rasheedat Sadiq, Wiehan de Jager
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences