

Abebe ya fara zuwa makarantar boko. Wannan ita ce shekararsa ta farko a makaranta.
Babansa manomi ne. Wata shekara baban Abebe ya shuka shinkafa a gonarsa.
Kowacce rana bayan an tashi daga makaranta, sai Abebe ya tafi gona domin ya taimaki babansa.
A gefen gonar su Abebe, akwai filin kwallo. Wani lokaci da yamma Abebe yana wasa da tsuntsaye, sai ga yaran turawa guda hudu sun zo za su yi wasan kwallo.
Yaran suka fara wasa. Kwallo tai tsalle ta fada cikin gonar shinkafa.
Kwallon ta bata shukar su Abebe. Daya daga cikin yaran ya ruga ya shiga cikin gonar shinkafa domin ya dauko kwallonsa, sai ya tattaka shukar shinkafar!
Daga nan yaran suka cigaba da wasansu. Kwallon kuma tai ta tsalle tana fadawa cikin gonar shinkafa.
Yaran kuma su ka yi ta tattaka shukar shinkafar domin su dauko kwallonsu. A duk lokacin da suka shiga, sai sun lalata wani bangare na shukar shinkafa.
Abebe da babansa ransu ya baci saboda lalacewar shukarsu.
Da Abebe da babansa babu wanda yake jin turanci. Ba su san yadda za su gaya wa yaran turawa su daina shiga cikin gonar suna bata musu shuka ba.
Su kuma yaran turawan ba sa jin kowanne yare sai turanci.
Baban Abebe ya ce, "Dana ka yi amfani da abin da ka koya a makaranta mana, ka gaya musu su daina jefa kwallo cikin gonarmu!"
Amma a wannan lokaci, Abebe bai iya komai ba sai haruffan A, B, C, D, E, F.
Abebe yana son ya yiwa yaran tsawa domin ya dakatar da su, amma bai san yadda zai musu magana da turanci ba.
Haka kwallon nan ta cigaba da tsalle a cikin gonar su Abebe. Daya daga cikin yaran ya rugo da gudu cikin gonar.
Abebe ya ruga da gudu wajen yaron yana daga masa hannuwansa. Ya fara yi masa tsawa iya karfinsa ya ce, "A, B, C, D, E, F!"
Ya kara buga musu tsawa har sau uku ya ce, "A, B, C, D, E, F!"
Baturen yaron ya tsaya da gudun da yake yi a cikin gonar. Abokansa su ma suka tsaya cak suna kallon Abebe.
Sai yaran suka yi magana da junansu da turanci suka yi murmushi. Domin sun fahimci abin da Abebe yake kokarin sanar da su.
Yaron dake rike da kwallon ya taka a hankali ya fita daga cikin gonar.
Sai yaran turawan su hudu suka tafi nesa da gonar su Abebe suka cigaba da wasansu.
Baban Abebe ya yi mamaki sosai. Ya gamsu cewa lallai dansa yana jin turanci.
Ya ce, "Lallai dana kana da kokari da fahimta!" Sai ya yi alfahari da dansa.
Abebe ma kansa ya yi mamaki kuma ya ji dadi. Har ma ya rasa abin da zai ce.
Baban Abebe ya cigaba da karfafa masa gwiwa a kan ya kara kokari a makaranta, domin ya cigaba da karatunsa idan ya kammala makaranta.

