Mutsuttsukakkiyar Kwarkwata
Zimbili Dlamini
Magriet Brink

A wani lokaci mai tsawo da ya wuce, an yi wasu matasa guda biyu waɗanda suka rasa shanunsu.

Sun yi ta neman shanun har zuwa yamma.

1

Da duhu ya kawo kai sai suka hango wani haske a wani gida.

Sai suka shawarta cewa su je su tambayi wajen kwana.

2

Suka ƙarasa zuwa gidan suka ƙwanƙwasa ƙofar. Sai kuwa ƙofar ta buɗe suka kutsa kai ciki.

Matasan nan ba su ga kowa ba, sai wata murya suka ji tana gaishe su.

3

Sai muryar ta ce da su, "Ni kwarkwata ce, ku buɗe tukunyar ƙarfen nan akwai abinci ku ci, sannan ga ruwa nan a cikin randa ku sha."

4

Sai kwarkwatar nan ta saka fatarta ta fice.

5

Matasan nan suka ci suka sha kuma suka yi godiya.

Sannan suka suka bar gidan.

6

Daga tafiyarsu, sai wani mummunan tunani ya zo musu cewa, "Ba zai yiwu ba a ce wai kwarkwata ce ta ba mu abinci."

Kawai sai suka shawarta cewa su koma su muttsuke wannan kwarkwatar.

7

Suka dawo gidan suka muttsuke kwarkwatar.

Kawai sai suka tarar babu kwarkwatar, kuma gidan ma ya ɓace.

Sai kuwa suka samu kansu a wani fili fetal.

8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Mutsuttsukakkiyar Kwarkwata
Author - Zimbili Dlamini
Translation - Fatima Shafi'u Abdulkadir, Mohammed Also
Illustration - Magriet Brink
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs