

Afeefah wata ƙaramar farar karkanda ce.
Masu taimako sun kawo mata agaji daga daji.
Mafarauta sun kashe mata mahaifiyarta.
Masu taimako sun kai Afeefah wani waje mai tsaro.
Zuciyar Afeefah ta karaya.
Sannan kuma tana tsoron kar mafarautan su dawo su ɗauke mata ƙahonta.
A hankali, Afeefah ta samu ƙawaye.
Ta ji ta samu tsaro, har ta yi wasa a cikin taɓo.
Kuma ta sha madara mai gina jiki a waje mai tsaro.
Wata rana sai Afeefah ta tambayi ƙawarta Aminaah. "Wai me ya sa suke son ƙahonmu ne?"
Aminaah ta yi wani huci ta ce, "Sun yarda wai ƙahonmu ana tsafi da shi."
Afeefah ta yi kuka ta ce, "To ai ƙahonmu ba na tsafi ba ne."
Sai Ameenah ta ce, "A'a tabbas ba haka ba ne, ƙahonmu daidai yake da gashi da farce."
Afeefah da Ameenah su ne na ƙarshen a irinsu.
Duk fararen karkanda sun kusan ƙarewa.
Kusan duka ma sun bar duniya.
Za mu iya ceto karakandai da kuma sauran dabbobin da suka kusa ƙarewa.
Me za ku iya iyi?
Ku nemo sauran.

