Sauro Mai Ban Haushi
Ursula Nafula
Magriet Brink

Кwan! Кwan!

1

"Waye a nan?" na yi tambaya cikin magagi.

2

"Ni ne," in ji wata murya mai rikitarwa.

3

"Kamar ya ni ne?" na tambaya.

4

"Na gaya maka dai ni ne," muryar ta sake faɗa.

5

"Ni ban san wani 'ni ne' ba," na ba shi amsa.

Na duba sai na ga sauro a maƙale a jikin gadona.

6

"Toh, sunana Sau," muryar ta amsa da ƙarfi fiye da da, har cikin kunnena.

7

"Wane Sau ɗin?" na tambaya lokacin da nake duba ƙarƙashin gidan saurona.

8

"Sau…ro." A ƙarshe ya faɗa. Kawai sai na ji cizo a kunnena.

9

"Ah! Na yi tsalle na fara dubawa. "Za ka yi da na sani." Na faɗa da ƙarfi.

10

Cikin fushi na tashi daga kan gado, na kunna fitila.

11

Tun daga nan na ƙulla yaƙi da sauro mai abin haushi!

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Sauro Mai Ban Haushi
Author - Ursula Nafula
Translation - Mohammed Also, Sanusi Hussain Kano
Illustration - Magriet Brink
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences