Ah! Кwallon ƙafa
Stella Kihweo
Onesmus Kakungi

Ina son yin wasa da abokina Chuma.

1

Mu abokanan kirki ne.

Duk sanda aka aiki ɗaya daga cikinmu, tare muke zuwa.

2

Wata rana, sai kakata ta aike ni shago don na siyo gishiri da man girki.

Sai muka tafi tare da Chuma.

3

Muna cikin tafiya, sai muka ga abokanmu suna buga ƙwallon ƙafa.

4

"Kai! Кwallon ƙafa!" Na faɗa.

Ni ma ina son na yi wasan.

5

Sai na ce da Chuma, "Mu tambaye su ko za mu iya yin wasan tare. Don ni ina son ƙwallon ƙafa sosai."

6

Sai Chuma ya ce, "Mu fara zuwa shagon, sannan sai mu dawo mu yi wasan."

7

Amma sai na ce, "Mu fara yin wasan! Don kaka ba za ta bar mu mu dawo ba."

8

Sai muka shiga abokanmu don yin wasan. Ni ne mai tsaron raga.

Turakun ragar an yi su da manyan duwatsu guda biyu.

9

Na yi ƙoƙari matuƙa wajen kama ƙwallon.

Don haka abokaina ba su samu damar zura ƙwallo ko ɗaya ba.

10

Muka yi ta wasa har sai da filin ya cika da yashi.

11

Sannan sai muka tafi shagon, amma kuɗin kaka sun ɓata! Sai na fara kuka.

Sai Chuma ya daka min tsawa, "Ka daina kuka, ai kai ne ka ce a fara yin wasan da farko."

12

Sai muka koma gida babu gishiri babu man girki.

Ga shi mun yi datti sosai, hankalinmu ya tashi.

13

Kaka ta fusata san da muka koma gida.

Abin da ta fara tambaya shi ne, "Ina kuka shiga duk tsawon wannan lokacin?"

14

A dole muka faɗa mata gaskiya.

Sai ta gargaɗe mu cewa, "Kar ku ƙara zuwa wasa ba tare da izini ba."

15

Sai muka tafi domin bai wa agwagi abinci.

Daga baya kuma muka wanke jikinmu.

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Ah! Кwallon ƙafa
Author - Stella Kihweo
Translation - Mohammed Also
Illustration - Onesmus Kakungi
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences