

Fati yarinya ce karama wanda ke gudu kamar
iska.
Tana son yin dariya kuma tana qoqari
Kaman yadda aka umarce ta.
Yau ranar wassanin makaranta ne.
Fati na wasan kwallon qafa
kuma tayi wasannin gudu kashi uku.
Bayan makaranta, ta tafi gida tare da baban qawan
ta Hawa.
Hawa ta ce, “Fati, ki na gudu da sauri!”
Fati ta iso gida ta tarar da mamanta tana
shirye-shiryen abinci.
Ta ce, “Mama, ina ini.”
Maman Fati ta amsa, “Ina ini. Yaya kike?”
Fati ta ce, “Yau mun yi wasannin makaranta. Na
yi gudu sosoi.
Ina jin zafi, na gaji kuma ina jin yunwa.”
Mama ta yi dariya, “Ta ce yar lele Fati na, an
haifeki da saurin qafa!”
“zan yi miyan kuvewa
kuma abinci zai nuna bada daxewa ba.”
Mama ta sa dan man ja a cikin baban tukunya ta
aza bisa wuta.
Lokacin da manjan ta yi zafi, sai ta yanka
albasa da tafarnuwa ta kuma juya kayan miyan har ya yi laushi.
Sai ta sa barkono, tumatiri da dan ruwa. Sai
kuma ta kara qwayan naman SA guda
shida.
Mama ta ce, “Fati, ki kula ki dinga juya
miyan.”
Fati ta ce, “ Toh, mama.”
Fati ta juya miyan sau xaya.
Sai tace, “Miyan na kamshin daxi.”
Fati ta juya miyan sau biyu.
Sai tace, “Wannan miyan da xanxanon
daxi.”
Fati ta juya miyan sau uku.
Sai tace, “Wannan miyan gaskiya da daxi!”
Fati ta kalli maman ta.
Mamanta ba ta kallon ta. Tana yankan alaiho da
za ta sa a miya.
Fati ta dauki kwayan nama xaya
daga tukunyan miyan ta ci.
“Mmm,” ta ce.
Sai Fati kuma ta dubi mamanta.
Mamanta ba ta kallon ta. Tana yanka kwai da za
ta haxa cikin miyan.
Fati da wuri ta dauki nama na biyu daga cikin
tukunyan miyan ta ci.
“Mmm. Mmm,” ta ce.
Fati ta kuma duban mamanta.
Mamanta ba ta kallonta. Tana yankan kuvewa
da za ta haxa a miyan.
Fati da wurwuri ta xauki
nama na uku daga cikin tukunyan miya ta ci.
“Mmm. Mmm. Mmm!” Fati ta ce.
Mama ta zo bakin murhu da koren ganye, da kwai
da kuvewa.
Fati na nan rike da baban chokalin katako.
Mama ta yi murmushi, “Na gode da juya wannan
miyan Fati.”
Fati ba ta san abin da za ta ce ba.
Mama ta sa koren ganye, kwai da kuvewa
a cikin miya.
Ta karbi chokali daga hannun fati ta fara juya
miyan.
Mama ta kalli cikin tukunyan miyan. Tana ganin
miyan na tafasa a kan wuta.
Mama tana neman kayan nama shida da ke cikin
tukunyan miyan.
“Xaya, biyu, uku.” Mama
ta ga kwayan nama uku kawai a cikin tukunyan miyan.
Mama ba ta ce komai ba. Fati ba ta ce komai
ba.
Da mama ta raba abinci, Fati bata samu nama
ba.
Fati ta ce, “Mama, yi haquri.
Ba zan qara yi ba.”
Ba ta qara yi ba. Wannan shi
ne qarshe.

