

Ko da yaushe, Damisa na qoqari ta kama Barewa
kuma Barewa na tsere ma Damisa
ko da yaushe
Wata rana, Damisa ta kira Barewa,
“mu zama abokai. Abin da ki ke ci ba na ci. Babu wani abu
da zai sa mu gaba.”
Barewa ta yarda. Don haka
Damisa ta ce, “Bari mu ranste don mu zama abokai. Idan kowane xayan mu ya karya
rantsuwar, yaro zai mutu.”
Su ka rantsai
don zama abokai. Da dare, Barewa tayi bacci a gindin bishiya. Damisa tayi bacci
a kan rassan a sama.
Ba da daxewa
Barewa ta yi qiba. Damisa ta sirance.
Damisa ta yi qwaxayin cin Barewa. Ta fada ma kanta, “ban damu da rantsuwar ba. Ba ni da yara!”
Damisa ta yi tselle zuwa kasa don kama Barewa. Amma ta maqale tsakanin
rassan biyu.
Barewa ta gigice. Ta yi tsalle ta fashe da kuka, “Beh! Beh!”
Damisa ta yi roqo, “Aboki na, taimake
ni. Mun yarda cewa duk
wanda ya karya rantsuwar mu ta zama abokai, zai rasa yaro.”
Barewa ta amsa, “ ya kamata mahaifin ki ce
ta yi rantsuwar. Yanzu ta zama na ki!”

