Damisa da Barewa
Magabi Enyew Gessesse
Isaac Okwir

Ko da yaushe, Damisa na qoqari ta kama Barewa.

1

kuma Barewa  na tsere ma Damisa ko da yaushe.

2

Wata rana, Damisa ta kira Barewa, "mu zama abokai. Abin da ki ke ci ba na ci. Babu wani abu da zai sa mu gaba."

3

Barewa ta yarda. Don haka Damisa ta ce, "Bari mu ranste don mu zama abokai. Idan kowane xayan mu ya karya rantsuwar, yaro zai mutu."

4

Su ka  rantsai
don zama abokai. Da dare, Barewa tayi bacci a gindin bishiya. Damisa tayi bacci
a kan rassan a sama.

5

Ba da daxewa Barewa ta yi qiba. Damisa ta sirance.

6

Damisa ta yi qwaxayin cin Barewa. Ta fada ma kanta, “ban damu da rantsuwar ba. Ba ni da yara!”

7

Damisa ta yi tselle zuwa kasa  don kama Barewa. Amma ta maqale tsakanin
rassan biyu.

8

Barewa ta gigice. Ta yi tsalle ta fashe da kuka, “Beh! Beh!”

9

Damisa ta yi roqo, “Aboki na, taimake
ni. Mun yarda cewa duk
wanda ya karya rantsuwar mu ta zama abokai, zai rasa yaro.”

10

Barewa ta amsa, “ ya kamata mahaifin ki ce
ta yi rantsuwar. Yanzu ta zama na ki!”

11
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Damisa da Barewa
Author - Magabi Enyew Gessesse, Elizabeth Laird
Translation - Amina Jibril, Joshua Abdul, Mariam Adamu, Muktar Agbadi
Illustration - Isaac Okwir
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences