Damisa da Barewa
Magabi Enyew Gessesse
Isaac Okwir

Damisa koda yaushe tana qoqarin kama barewa.

1

Barewa kullum na kuɓuta daga tarkon damisa.

2

Wata rana, Damisa ta kira Barewa, ''Zo mu zama abokai. Abun da kike ci, ni bana ci. Babu dalilin yin gaba.''

3

Barewa ta amince. Sai damisa ta ce, ''Mu yi rantsuwa don zama abokai. Idan ɗayanmu ya saɓa alƙawari zai mutu.''

4

Suka yi rantsuwa ta zama abokai. Barewa ta kwanta ƙarƙashin bishiya, damisa kuma a kan rassan bishiya.

5

Jim kaɗan barewa ta yi ƙiba, damisa kuwa ta rame.

6

Damisa ta yi kwaɗayin cinye barewa. Don saɓa rantsuwa da tunanin bata da ɗa.

7

Damisa ta yi tsalle domin kama Barewa. Sai ta maƙale a tsakanin rassa biyu.

8

Barewa ta tsorata. Ta buga tsalle tana kuka, ''ɓeh! ɓeh!''

9

Damisa ta yi roƙon cewa, ''Ƙawata, taimaka mini. Mun yi rantsuwa kan duk wanda ya karya alƙawari zai rasa ɗa.''

10

Barewa ta amsa, ''Iyayenki ne suka yi rantsuwa.'' Yanzu matsalar ki ce.

11
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Damisa da Barewa
Author - Magabi Enyew Gessesse, Elizabeth Laird
Translation - Hamza Usman Shehu, Muhammad Tijjani Ibrahim
Illustration - Isaac Okwir
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences