

Wata rana ɗan taure da ɗan damisa suka ƙulla abota.
Ana nan, sai suka tafi daji don su yi wasa.
ÆŠan taure da É—an damisa suka yi dare sosai kafin su dawo gida.
Sai É—an taure ya ce wa innarsa, "Yau na haÉ—u da wani aboki mai kirki. Gobe ma za mu sake haÉ—uwa da shi."
Sai innarsa ta ce, "Wannan ba abokinka ba ne, yau ma na gode wa Allah da ka dawo lafiya." Don haka, kada ka je wurinsa gobe.
Shi ma É—an damisa ya faÉ—a wa innarsa cewa, "Na haÉ—u da wani aboki mai kirki. Gobe ma zamu sake haÉ—uwa da shi."
Damisa ta cika da mamaki. sannan ta ce, "Dana, me ya sa ba ka cinye shi ba? idan kun haÉ—u gobe kar ka dawo gida sai ka cinye shi."
Washegari, sai ɗan damisa ya tafi ƙauyensu ɗan taure yana nemansa wurjanjan.
Amma ɗan taure ya laɓe a bayan innarsa. Ya ƙi fitowa daga gida.
Ɗan damisa ya taƙarƙare yana cewa, "Abokina, abokina fito mana mu yi wasa!"
Ɗan taure ya numfasa ya leƙo, sannan ya ce, "Innata ta faɗa min kai ba abokina ba ne, hanyar jirgi daban da ta mota," ni kuma ina jin maganar innata.
Don haka, jikin É—an damisa ya yi sanyi, ya juya gida cike da takaici.

