Zomo Da Kura
Dennis Mulwa
Wiehan de Jager

A wani lokaci can daya shude, dabbobi sukan yi magana. Zomo da kura sun zauna a wani wuri.

1

Sun yi abuta tare. Suna komi tare, har ma a wajen neman abinci.

2

Zomo na da wayo kwarai. Yana tara abinci da yawa fiye da kura.

3

Ita ko wannan kura, ragguwa ce, kuma tana son cin abinci kwarai. Koda yake yanayin farautarsu ya banbanta, sun hada abincinsu tare.

4

Zomo yana amfani da hikimarsa wajen neman abinci da sauri. Kuma ya kan ci kafin ya kawo sauran a wurin da kura take.

5

A lokacin fari, yana da wuya su biyun su tara isasshen abinci da kansu.

6

Sai kura ta bar neman abinci. Ta dogara akan dan abinda Zomo ya samo ya kawo gida. Wannan yasa Zomon nan ya ji yunwa da bakin ciki. A lokacin da zomo ya dawo babu abinci, sai taji jikinta yayi sanyi.

7

To amma kuran nan bata nuna alamar zata canza daga halinta na dogaro akan dan abinda Zomon nan za ya tara masu. Rayuwa ta zamo mai wuya saboda Zomo baya iya ciyar da su. Don haka sai Zomon nan ya kuduri ya nemo hanyar rabuwa da wanna kura.

8

Wata rana kura ta farka da sassafe. Sai suka fara shawarar yadda zasu rayu.

9

Tattaunawarsu bata kare ba saboda banbancin ra'ayoyi. Kuran nan tace bata iya samo komai saboda bata iya gudu sosai kamar zomo. Saboda haka zata zauna tayi aikin gida.

10

Da yamma Zomo na farauta, sai yaga danyun 'ya'yan ruman. Ya zauna dan shirya yadda zai kwashe su ya kai gida. Abin da wuya saboda gonar na da shinge.

11

Tare da sa himma, Zomo ya kai gabishiyar. Ya hau ya debo masu yawa. Ya ci kuma ya tattara sauran ya sa a kwando, ya dauka. Sai yaji gajiya saboda ya cika cikinsa sosai. Sai yace bari in dan huta, kawai barci ya dauke shi. Sai ga mai gona ya rutsa shi ya daure shi da igiya ya tabbatar baya iya gudu.

12

Igiyar na da tsayi kwarai, zomo ya ta ja har yakai inda kura take. Yace mata akwai wata liyafa shi yasa aka daure ni da igiya mai tsawo don kar in bata hanya.

13

Sai sakaran kuran ya kwance zomon nan ya daure kanshi, ya yi ta bin igiyar har ya tarad da mai gonar a fusace yana jiran isowarsa yana rike da wata shareriyar wuka. Aka yanke kuranan take, aka ba karnukan mai gona suka cinye, sannan aka yi mutum-mutumi da fatar kuran.

14
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Zomo Da Kura
Author - Dennis Mulwa
Translation - Ibrahim Musa
Illustration - Wiehan de Jager, Rob Owen
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs