Muna Iya Kirga Kyanwoyinmu
Nina Orange
Jesse Breytenbach

Kyanwa nawa ne? Babu kyanwa ko guda. Ba kyanwa.

1

Kyanwa nawa ne? Kyanwa daya ce. Baƙar kyanwa na iya cin jan nama.

2

Kyanwa nawa ne? Kyanwa biyu ne. Fara da ruwan toka. Farar kyanwa da ruwan toka suke wasa a cikin furanni da kuma kan dabe.

3

Kyanwa nawa ne? Kyanwa uku. Toka-toka, madara-madara, ɗabbare-ɗabbare. Suna wasa sama da ƙasan bango.

4

Kyanwa nawa ne? Kyanwa huɗu. Kyanwa huɗu abokan Ali ne.

5

Kyanwa nawa ne? Kyanwa biyar. Kyanwa biyar na ta wasan kai-kawo a ɗakin hutawa. Ina son haka.

6

Kyanwa nawa ne? Kyanwa shida. Kyanwa shida suna iya zama tare su kalli fim.

7

Kyanwa nawa ne? Kyanwa bakwai. Kyanwa bakwai na wasa a tsakar gida.

8

Kyanwa nawa ne? Kyanwa takwas. Kyanwa basa son karnuka.

9

'Yar kyanwa ta maƙale a kan bishiya! Ali ya ce, "Zan ceto ki."

10

"Inna ko mu ajiye shi? saura daya tal." Kyanwa nawa ne? Inna tace kyanwa tara sun yi yawa.

11
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Muna Iya Kirga Kyanwoyinmu
Author - Nina Orange
Translation - Aisha Muhammad
Illustration - Jesse Breytenbach, Jesse Pietersen
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First sentences