

Gatanan, Gatananku.Wani yaro ne da kakarsa ke matuƙar ƙaunarsa. Da zai tafi sai ta ba shi kyautar ƙwai ta ce masa, "Daga wannan ƙwan za ka samu dukiya mai yawa da za ka yi aure idan ka girma."
Yana fita sai ya haɗu da masu cirar kanya, sai suka roƙe shi da ya ba su aron ƙwan, su yi amfani da shi don kaɗar kanya. Suna jefawa sai ƙwan ya fashe.
Yaro ya yi ihu ya ce, ''La! La! La! Sai kun biya ni ƙwai na da kakata ta ba ni domin ya zamo silar aurena.''
Sai suka ɗauki sandar da suke amfani da ita suka ba shi. Daga nan sai ya tafi.
Daga nan, sai ya haɗu da wasu magina. Suka buƙaci aron sandarsa. Suka yi amfani da ita wajen gina gida. A ƙarshe suka kakkarya sandar.
Yaron ya yi kuka ya ce, ''Kai! Kai! Kai! Sai kun biya ni sandata da masu kaɗar kanya suka ba ni. Yayin da suka karɓi ƙwai na da kakata ta ba ni, domin ya zama silar aurena.''
Sai suka ba shi ciyawar rufin ɗaki. Daga nan sai ya tafi.
Daga nan sai yaron ya haɗu da wani mai kaɗar kanya, wanda ya roƙe shi da ya ba shi ciyawarsa don ya ba shanunsa su ci.
Yaron ya yi kuku ya ce, ''Ah! Ah! Ah! Ka sani cikin damuwa. Ciyawar ba tawa ba ce, ta masu kaɗar kanya ce. Ba haka kawai maginan suka ba ni ita ba. Sun karya mini sanda, kuma ba tawa ba ce, ta makiyaya ce. Sun bani ita ne a madadin ƙwai na. Kuma ƙwan ma ba nawa ba ne, na kakata ne da ta bani a matsayin sadakin aurena.''
Makiyayi ya ba wa yaro saniya. Yaron ya tafi da saniya.
A hanyarsa ta komawa gida ne, yaron ya haɗu da masu bikin aure. Iyayen amarya suka nemi ya ba su saniya. Sai ya ba su. Su kuma suka yanka, suka cinye.
Yaro ya fashe da kuka, "Um! Um! Um! Kun sanya ni cikin matsala! Saniyar ba tawa ba ce. Ta makiyayi ce. Ya bani a madadin ciyawata. Ciyawar ba tawa ba ce, ta magina ce. Sun bani ita saboda sandata da suka kakkarya. Sandar ma ba tawa ba ce, ta makiyaya ce da suka bani a madadin ƙwai na. Kwan ma na kakata ne, wanda ta bani domin samun sadakin aure."
Sai dangin amaryar suka ce, ''Babu abin da za a yi sai mu biya ka. Bari mu baka amarya.'' Ya tabbata, ''Alheri danƙo ne, ba ya faɗuwa ƙasa banza.''

