

An dauki lokaci ana tsamanin saukar ruwa sama, don haka jama'a suka taru a kofar gidan Liman don a fita rokon ruwa.
Yayin da Liman ya fito ya roki Allah ya ba da damina mai albarka, da kuma fatan samun amfani gona mai kyau.
Washegari yara na wasa a waje,sai gagarimin hadari ya taso daga gabas, da alamun za a samu ruwa.
Ganin cewa an yi rokon ruwa, ga shi kuma hadarin ya hadu sosai don haka mahaifiyar yaran ta ce, su shigo gida.
Daga nan sai aka tsuge da ruwa
Mun yi farin cikin samun ruwan farko, sai dai murna ta koma ciki, don ruwan ya dade bai tsagaita ba.
Ruwa ya malale koina, har ya tafi da gadar da ta hada kauyenmu da cikin birni.
Gyara ya zamo anoba a gare mu,domin ruwa ya mamaye gidaje da dama.
Jama'ar karkararmu sun shiga damuwa,kasancewar ruwan ya shafe gonaki da gidajensu, ga shi uwa uba ma gadar garin ta rushe.
Wani abin ban tsoro kuma sai ga Kada na iyo a saman ruwa, wannan ya sa jama'a suka kidime gaba daya.
Don haka duk wata harka ta tsaya, yara ba damar zuwa makaranta, sakamakon yadda ruwan ya mamaye koina
Wannan annoba ta haifar da damuwa ga limami tare da al'ummar garin.

