

Wahala na cikin ɓangaren rayuwar kowace halitta. Karnuka da ƙadangaru suma abin halitta ne. Kare da Kadangare abokan juna ne na kusa. Suna tattaunawa a kan matsalar rayuwa sai ƙadangare yace "Na sha walaha fiye da kai". Kare ya amsa masa 'Ba ka ga yadda nake shan wahala ba lokacin neman abinci"?. Ƙadangare yace "Duk lokacin da zan ci Ƙudaje sai su tashi sama, rayuwata tana ƙunci, ko da yake wani lokaci ina laɓewa a jikin bango, saboda domin in samu sa'ar ƙudajen.
Suna cikin magana sai ga wasu mutane za su ci abinci, sai ƙadangare ya maƙale yana kallon su. Shi kuwa kare ya matso kusa da su. Sai suka kore shi tare da duka, ya kuka whoo! whoo!. Kare ya kasa gudu saboda yunwa, sai ya dawo saboda abincin. Sai aka jefa masa abincin ɗankaɗan a fako mai tsananin datti. Ƙadangare yana maƙale a kan bango ya na kallon duk abin da yake faruwa. Ƙadangare ya gyada kansa kaf! kaf!kaf! yace "Lalle kare na shan wahala sosai.
Wanna shi ne dalilin da ya sanya duk inda ƙadangare ya ga kare ya ke girgiza kansa. Shi ne ma ƙadangare ya fahimci cewa abinci wani gubar wani. Ka da ka kambama matsalarka akan ta wasu,, za su iya zama sun fi ka matsala kuma su yi maka dariya.

