

Wata yarinya iyayenta suka aike ta wajen kakanta da ya ke zaune a cikin daji. Ta tafi cikin farin cikinta.
Lokacin da ta isa kusa da daji, ta haɗu da wata akuya ta yi mata magana cewa ta yi a hankali domin za ta haɗu da namun daji.
Lokacin da ta kai tsakiyar dajin, ta samu namun daji da yawa a kusa da hanya, sai ta yi ta gudu tana ƙara.
Bayan ta fita daga daji, sai ta haɗu da tsuntsaye masu yawa a waje guda suna ƙara, sai ta ƙara gudu tana ƙara. Sai kakanta ya jiyo ta.
Kakanta ya ce da matarsa wannan jikarsu ce. Ya fita da sauri tare da karensa domin duba ta kuma ya same ta a gajiye.
Lokacinda suka isa ta shiga gida ta gaishe da sauran yara kuma ta ɗauki abinci. Bayan ta gama cin abinci ta ba su labarin abin da ya faru a kan hanya.
Bayan fadɗn abinda ya faru sai aka ba ta shawara ka da ta ƙara biyowa ta cikin daji ba tare da wani ba, sai ta tafi cikin farin ciki sukai ta wasa da sauran yara.
Ba ta sake biyowa ta cikin dajin ba tare mai rakkiya ba.

