

Wata rana an aiki Musa, Garba da Kande wajen tsinto itacen girki a daji. Dajin ya na da haɗari. Kakarsu ta gargaɗesu kar su yi wasa wajen ɗebo itacen.
Dajin ya na da nisa sosai daga gidansu. Mahaifiyarsu ta kan je da su dajin, amma ranar ta je kasuwa sayen kayan lambu.
Da suka je dajin ba su dawo da wuri ba. Babbarsu ta dawo ta damu da ba ta gansu ba. Saboda haɗarin dajin mutane su na maganarsa. Dajin cike yake da macizai masu haɗiye mutane da Awaki.
Lokacin da za su bar gida an gargaɗesu da kada su shiga cikin dajin sosai. Amma Kande da yake ba ta jin magana ta yanke shawarar shiga ciki sosai. Ta shawarci 'yan'uwanta su shiga tare amma suka ƙi. Ta faɗa musu ta ga itace mai yawa a karan farko da ta je, amma suka ƙi.
Kande ta kan yi abinda aka hanata kowane lokaci. Lokacin da ta ke neman itace sai ta haɗu da wani mutum da ke zaune cikin dajin ya ce mata zai nuna mata inda za ta sami itace mai yawa. Ta kira 'yan'uwanta su tafi tare, sai suka tunatar da ita cewa an gargaɗesu cewa "kar su yiwa kowa magana a cikin daji" amma kawai ta yanke shawarar tafiya.
Musa da Garba sun ɗaure itacensu, sun jira 'yar'uwarsu har sun gaji, amma ba ta zo ba; sai suka tafi suka barta. Lokacin da suka isa gida sai mahaifiyarsu ta tambaye su "Ina Kande"? Suka ce ba su san inda take ba. Maharbi ya ɗauki Kande zuwa gidansa yace ta kwana, gobe ya kaita gida saboda dare ya yi. Mutumin nan ya na zaune a cikin wani kogo tare da namun daji, Kande ta razana matuƙa amma haka ta kwana.
Tsakar dare sai Maharbi ya canja halittarsa, ƙafafuwansa dogaye da yatsu da yawa, kansa ya zamo babba da manyan idanuwa, ƙafafuwansa kamar na giwa. Sai Kande ta ƙara tsorata ta na so ta gudu da safe. Sai ta tuna cewa 'yan'uwanta sun gargaɗeta.
Mahaifiyarta ta ɗauki fitila ta tafi nemanta. Ta shiga cikin daji ta na kiran sunanta tana dubawa amma ba ta sameta ba. Kande ta yi ta yunƙurin gudowa amma Maharbi ya ce "Zai bar ta ne ta tafi kawai idan ta faɗi sunansa". A kullum Kande ta saurara ko mutumin nan zai fadi sunansa. Wata rana bayan ya sha giya sai ya ambaci sunansa "Agagasheshili" sunan ya yiwa Kande tsawo da ba za ta iya faɗarsa ba.
Kullum ta na kuka saboda ta na son tafiya gida amma ta kasa fadar sunan yadda yake daidai. Wata rana Ogre ya same ta tana kuka kuma ya tambaye ta "Mene ne dalilin kukanta"? Ta ce ta yi ta fadi sunan amma ba za iya fada ba. Lokacin da ya lura ta na ƙoƙarin faƙar sunansa sai ya canja zuwa maciji.
Maciji ya fara magana cewa ba wanda ya san sunansa. Kande ta ji tsoro sai ta fara gudu ba ta yi nisa ba aka haɗiye ta da rai. Danginta suka duba ko ina ba su ganta ba.'Yan'uwanta aka bar su cikin damuwa kamar yadda suke ƙaunarta. Cikin nadama suka ce za su bi umarni.

