Sanin Damisar Bunu
Abubakar Saidu-Sado
Philip Hayab John

A wani gari mai suna Magarya. An yi wani mutum mai suna Bunu.

1

A garin Magarya, masana labarai suke bada labarai masu qayatarwa.

2

Da aka zo kan Bunu, sai ya ce, "Labarina a kan Damisa ne."

3

Yana fadin kan labarinsa, sai kowa ya yi shuru ya kuma saurara.

4

Bunu ya gyara murya ya ce, "Damisa kamar Kyanwa ta ke."

5

Sai kowa ya ce, "Lallai, haka ne."

6

Kuma ya ce, "Damisa na da tsawon bindi."

7

Sai masu saurare suka ce, "Ummm, gaskiya ne!"

8

Lokacin da Bunu ya fahimci ya fara birge jama'a.

9

Sai ya yi farat kamar qorarren mai bada labari, ya ce, "Ai lokacin da muke yara, malamin mu ya kai mu bakin rafi ya nuna mana Damisa."

10

Ita Damisa tana da qaho biyu irin na Barewa.

11

Sai kowa ya kyalkyace da dariya yana yi masa ba'a.

12

"Bunu makaryaci ne, kuma bai san yanda Damisa take ba."

13

Bunu ya gane kuskuren sa sai ya ce, "Daga yau ba zan
sake ba da labarin abinda ban sani ba."

14
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Sanin Damisar Bunu
Author - Abubakar Saidu-Sado, Lawali Kaura, Philip Hayab John, Sani Masama Garba, Timothy Anche
Adaptation -
Illustration - Philip Hayab John
Language - Hausa (Nigeria)
Level - Longer paragraphs