

A wani gari mai suna Magarya. An yi wani mutum mai suna Bunu.
A garin Magarya, masana labarai suke bada labarai masu ƙayatarwa
Da aka zo kan Bunu, sai ya ce "labarina a kan damisa ne."
Yana faɗin kan labarinsa, sai kowa ya yi shuru ya kuma saurara.
Bunu ya gyara murya ya ce, "Damisa kamar Kyanwa ta ke."
Sai kowa ya ce "Lallai, haka ne".
Kuma ya ce, "Damisa na da tsawon bindi."
Sai masu saurare suka ce. "Ummm, gaskiya ne!"
Lokacin da Bunu ya fahimci ya fara birge jama'a.
Sai ya yi farat kamar ƙwararren mai bada labari, ya ce "Ai lokacin da muke yara, malamin mu ya kai mu bakin rafi ya nuna mana damisa."
Ita damisa tana da ƙaho biyu irin na barewa."
Sai kowa ya ƙyalƙyace da dariya yana yi masa ba'a.
"Bunu maƙaryaci ne, kuma bai san yanda damisa take ba."
Bunu ya gane kuskuren sa sai ya ce, "Daga yau ba zan
sake ba da labarin abinda ban sani ba.

