

An yi wata ƙaramar yarinya da ake kira Fati. Bayan rasuwar ma'aifin, Fati ta zamna tare da ma'aifiyarta. Wata rana, ma'aifiyarta ta ce mata, za ta ƙaura ta koma wani gari don ta sake wata sabuwar rayuwa.
Fati ko ba ta son barin garinsu, kuma sai ta yi ta kuka. Ma'aifiyarta ta ji tsoron barin ta ita kaɗai, saboda garin akwai ƙatti da suke ci. Amma Fati ta yi ta kuka har sai da ma'aifiyar ta yarda ta bar ta.
Ma'aifiyar ta ɗauki alkwalin kai ma ɗiyarta abinci kullum. "Zan yi waƙar da za ki gane ni in na zo. Amma kar ki buɗe ma kowa ƙofa," in ji uwar Fati.
Fati ɗiyata! Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki! Fati ɗiyata! Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki!
Washe gari, ma'aifiyar Fati ta zo ta kawo ma ɗiyarta abinci. Ta fara waƙa: Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fati ta buɗe ƙofa ta ci abincinta mai daɗi.
Ma'aifiyarta ta sumbace ta, kuma ta koma garinta. Fati ta koma ɗakinta ya kwanta. Ashe wani ƙato yana laɓe bayan wani icce, yana saurare Fati da ma'aifiyarta!
Lokacin da Fati ta kashe fitila sai ta ji wata babbar murya, na rera waƙar da ma'aifiyarta take bakin ƙofarta. Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! "Tafi ka ba ni wuri! Wannan ba ma'aifiyata ba ce," in ji Fati. "Kai ƙato ne!" ƙato ya tafiyar shi cikin ɓacin rai. Ya koma cikin gidanshi na dutsi.
Kullum safe da maraice, ma'aifiyar Fati tana kawo mata abinci. Kullum safe da maraice, ƙato ya na zuwa shi ma. Amma kullum Fati na korar shi. Tana gane shi ta babbar muryarshi lokacin da yake kokoyon waƙar.
Wata rana, ƙato ya yi tunani ya ce: "Ina iya sauya muryata don ta zama kamar ta ma'aifiyar Fati." Sai ya fura wuta da yawa kuma saka dutsi mai sulɓi cikin wutar. Bayan dutsin ya yi zafi, sai ya fiddo shi ya hadiye shi! "Gulugulu!" Dutsin ya wuce ta maƙogoron ƙaton.
Ƙato ya fara waƙa don ya ji in muryarshi ta sake.
Ya yi ta jin daɗi ya ji muryar tashi ta yi kama da ta ma'aifiayar Fati!
Washe gari, ƙato ya je bakin ƙofar Fati. Ya fara waƙar kamar haka: Fati ɗiyata! Fati ɗiyata! Fito maza ga abincinki! Fito maza ga abincinki!
Fati ta ji daɗi da ji muryar ma'aifiyarta. Da buɗe ƙofa, sai ga ƙato! Sai ta so ta rufe ƙofar amma ƙato ya fi ƙarfinta! Ya ɗauki Fati ya saka ta cikin buhu.
Ƙato ya nufi hanyar gidan shi na dutsi, kuma yana waƙar jin daɗi. "In dama ina da giyar burkutu, da na ji daɗin abincina da dare! Yau sai na ji daɗi!" yake faɗi.
Can da hantsi, ma'aifiyar Fati ta zo ta kawo mata abincin kamar yadda ta saba kullum. Ta rera waƙar, amma Fati ba ta fito ba. Ta sake rera waƙar, Fati ba ta amsa ba, shiru! Bayan na ukku, sai ta tura ƙofar. Babu Fati. Sai ta yi mamakin abin da yake iya faruwa, sai ta yi tunani da gaugawa don samun wata dubara.
Sai ta cika wata ƙwarya da giyar burkutu ta ɗaura saman kai, ta tafi wajen gidan ƙato kuma ta sallama mishi. Ƙato da ya ji ƙamshi burkuntun sai buɗe ƙofar ba da ɓata lokaci ba. "Ina wuni ƙato!" in ji ma'aifiyar Fati. "Ina wucewa na ji kana waƙa da kyau. Yanzu zan je wani garin wajen bikin zagayowar shekarar aifuwar wata ɗiyata."
Ƙato ba zay barin wannan damar da aka ba shi ta ya sha giyar burkutun! Sai ya sabkar da ma'aifiyar Fati gidanshi. "Bari in zuba maka giyar kafin in wuce." In ji ma'aifiyar Fati. Ƙato yana jin daɗi ya samu giya.
Ma'aifiyar Fati tana zuba mishi yana sha, yana ta sha sai da ya shanye duk ƙwaryar. Yanzu ƙato ya yi tilip! Yana yin maye har barci ya kwashe shi.
Lokacin da ma'aifiyar Fati ta ji ƙato ya fara shinkori, sai ta buɗe buhun suka gudu da ita da Fati. Fati da ma'aifiyarta sun gudu sun koma gida. Tun daga ranar nan, Fati take tare da ma'aifiyarta cikin sabon garinsu!

