ILIMI HASKE NE
Zainab Abdulkadir
Bashir Muhammad

A wani kauye mai suna kurawa, yawanci yara ba sa son karatu sai wasa.

1

Suna ganin zuwa makaranta ma wahala ce kawai. Saboda haka, za su wuni suna wasan su kawai.

2

Amma Allah da ikonsa, a cikin yaran wanan kauyen, akwai wata yarinya mai suna Zainab da ta fita daban.

3

Ita Zainab tana San zuwa makaranta da yin karatu sosai tun tana karama.

4

KO a makaranta idan babu malami a aji, ita Zainab za a tarar tana karatun littafinta kawai.

5

A gida Kuma, ta kan yi amfani da fitila da dare don tayi karatu.

6

Wata rana anyi ruwan sama sosai da ya lalata gonakin dagidajen mutanen kauyen.

7

Mutanen kauyen sun shiga damuwa, fargaba da tsoro a dalilin wannan iptila'in ruwan sama.

8

Nan take, Zainab ta tuna da abinda ta koya a makaranta da shapi irin wadannan abubuwan.

9

Ta tattara yaran mata na wanan kauyen ta koya musu yadda za su rubuta korafi akan abinda ya faru.

10

Suka tura wasikar korafin zuwa ga hukuma don a tallafawa mutanen wanan kauyen.

11

Bayan wani dan kankanin lokashi, aka turo taimako daga hukuma zuwa wannan kauyen

12

An gyara rijiyoyi, an bada kayan abinci, Kuma an bada iri na keuta.

13

Mutanen kauyen suka yimmamaki ganin aikin da aka musu Kuma sunji dadi.

14

Yaran kauyen suka gane ILIMI na da matukar amfani. Su ma suka fara zuwa makaranta da Zainab.

15

Kuma tun daga ranar ko wani wayewan gari, yaran da suke zuwa makaranta daga wanan kauyen karuwa suke. Tabbas ILIMI na da matukan amfani

16
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
ILIMI HASKE NE
Author - Zainab Abdulkadir
Illustration - Bashir Muhammad
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs