AMINU YARO MAI LURA
Amina Abubakr
Bashir Muhammad

Akwai wani yaro mai suna Aminu a wani kauye.

1

Aminu yana son karatu da tambaya abubuwan masu amfani. Yana yawan lura da abin da ke faruwa a kusa dashi.

2

Wata rana, Aminu ya lura da hayaki yana fitowa daga daji. Yawanci mutane sun dauka hayaki na na manoma.

3

Aminu ya ga wuta tana kara karfi. Ya gudu zuwa kauye ya fada wa manyan gari abinda ya gani a daji.

4

Wasu sun yi shakkar abin da Aminu ya fada, amma ya nace da gaske yake.

5

Daga baya aka je aka ga wutar tana daf da shiga kauye.

6

Mutanen kauyen suka hada kai domin kashe wutar

7

An ceci gidaje da gonaki da dabbobi

8

Shugaban kauyen ya yabawa Aminu. Hankalin Aminu da nutsuwar sa sun ceci kauye.

9

Daga wannan ranar, yaran kauyen suka kasance suna kwaykwayon halin Amina na lura.

10
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
AMINU YARO MAI LURA
Author - Amina Abubakr
Illustration - Bashir Muhammad
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs