AMALALA
Shuaiba Adamu
Babangida Ibrahim

A wani lokaci daya yawuce. Anyi wani yaro mai suna Babangida. Babangida ya kasance ba shida kyawun hali domin kullum ba shi da aiki sai yi wa yara 'yan uwansa mugunta ga shi Da stokana da kuma keta.

1

Idan wani abin bacin rai ya samu wani Daga cikin yara, Sai Babangida ya yi ta mass dariya Yana stokana.

2

Malamar su Babangida ta sha yi masa faɗa. Amma Babangida ba ya Jin maganarta, domin ya raina duk nagaba da shi.

3

Wata rana Babangida Yana cikin aji tare dasauran yara Suna daukar darasi Sai fistari ya kama Babangida.

4

Babangida ya nemi izini malamarsu domin ya je ya yi fistari, Amma Sai malamar ta hana Shi fita. Domin ta dauka Babangida Yana yin shakiyanci ne Kamar yadda ya saba.

5

Sai Babangida ya sake neman izini a wajen malamarsu. Amma malama ba ta ba shi izini ba. Ga shi Kuma fistari ya maste Shi.

6

Can Sai Babangida yakasa jurewa har yayi fistari a wando ya bata wandonsa kuma ya bata wajen zamansa.

7

Ko da sauran Yara suka ga abin da ya Samu Babangida sai suka fashe da dariya, suka yi ta nunashi suna stokanar sa. Har ma suka fara yiwa Babangida Waka, Suna cewa "Amalala Mai fistarin zaune" Sai Babangida ya fashe da kuka.

8

Koh da malamar su Babangida ta ga abin da yake faruwa, sai ta stawatar wa Da sauran Yara, ta Kuma yi musu gargaɗi a kan stokanar Babangida

9

Sai malama ta bai wa Babangida izini domin ya je ya wanke jikinsa, Babangida ya ji kunya sosai a ranar. Kuma ya ji ba dadi a lokacin da yara suke stokanar sa.

10

Sai Babangida ya faɗa a ransa cewa "Au a she haka yara suke ji idan na ci zarafinsu koh na stokanesu?"

11

Tin daga ranar Sai Babangida ya chanja halayensa ya kuma yi alkawarin ba zai sake yin stokana da cin zarafin wani ba.

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
AMALALA
Author - Shuaiba Adamu
Illustration - Babangida Ibrahim
Language - Hausa (Nigeria)
Level - First paragraphs