

A zamanin da, kura da gizo sun zauna a gida ɗaya. Kowannensu yana fita neman abinci da safe sai dare zai dawo.
Duk san da gizo ya fita yakan dawo da abinci mai yawa, amma ita kuwa kura, takan dawo babu komai.
Rannan bayan sun dawo,sai kura ta roki gizo ya taimaka mata da abincin dare. Sai gizo ya bata abinci ta ci ta ƙoshi.
Sai kura ta ce, "Don Allah a ina kake samo abinci haka ? Don ni ma na dinga bin ka."
Sai gizo ya ce, "Ke ba ɗa ki iya jurewa ba. Kawai ki bari ɗan dinga san miki."
Kura ta dage cewa ɗa ta iya. Da gari ya waye, sai gizo ya tashi ya tarar kura ta shirya tsaf tana jiran sa ya tashi su tafi.
Sai suka yi doguwar tafiya kafin suka tarar fa woni ƙaton gida. Sai gizo ya ce, "Balan." Sai ƙofar gidan ta buɗe.
Suna shiga, gizo ya ce, "Zargagum-gum." Sai ƙofar ta rufe. Sai ga kayan abinci iri-iri. Suka ɗiba da yawa sanan suka tafi.
Da suka dawo sai kura ta ce, "Ka bari daga yau ni zan dinga zuwa ɗibo mana abinci, kai kuma ka zanna ka dinga dafa mana mu shi."
Gizo ya amince, amma ya gargaɗi kura da ta Kula sosai domin gidan na wani dodo ne mai iya dawowa a kodayaushe.
Da Kura ta zo gidan dodo washegari, sei ta ce, "Bilan," ƙofa ta buɗe. Ta shiga ta ce, "Zargagum-gum," ƙofa rufe.
Ta ɗibo kayan abinci a buhu amma day ta zo fita, sai ta manta me ake faɗa ƙofa ta buɗe. Ta na cewa zargagum-gum ƙofar na ƙara rufewa.
Da Kura ta rasa hanyar fita, hankslin ya tashi tana kuka. Can da yamma ga dodo ya dawo ya samu kura a tsungune.
Ya ce, "Yawwa yau na kamo mai yi min sata. Zan dafa ki na cinye ki." Kura ta ƙara fashewa da kuka tana roƙon sa ya yi haƙuri.
Kura ta yi wa dodo alƙawari ba za ta sake yin sata ba idan ya ƙyale ta. Dodo ya ƙyale ta tafi bai mata komai ba.
Da ta je gida sai ta ba wa gizo labari duk abin da ya faru. Sai gizo ya tsorata. Daga nan sun daina satar kayan woni Kuma.

