MAI RAINuWA
Ibrahim Abba
Ibrahim Abba

An yi woni mutum talaka Mai yawan rainuwa. Duk abin day aka ba shi, sai ya ce ya yi masa kaɗan.

1

Yana da wata kaza guda ɗaya. Sai ya ce, "ni wannan kaza me Zan yi DA ita. Guda ɗaya tayi min kaɗan. Ina ma da ina da kaji ɗari."

2

Dan haka, ya ce zai yanka kazar nan.

3

Sai kazar ta roƙe shi da kada ya kashe ta. Tace za ta dinga yi masa ƙwai Na gwal kulum guda ɗaya.

4

Washe gari kaza ta cika alƙawari. Tayi masa ƙwan gwal guda ɗaya. Ya je kasuwa ya siyar ya samu kuɗi Mai yawa.

5

Ranan Sai mutumin nan ya ce shi ba ya son ƙwai guda ɗaya kulum don ya yi masa kaɗan. Dan haka, zai yanke wanan kazar don ya kwashi duk gwan da yake cikinta.

6

Bayan ya yanke kazar, Sai ya gan babu komai a cikinta banda kayan cikinta.

7

Daga nan, kawai Sai mutumin nan ya Fara kuka. Kuma Daga nan, ya koma talaka, bai ƙara yin arziƙi ba.

8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
MAI RAINuWA
Author - Ibrahim Abba
Illustration - Ibrahim Abba
Language - Hausa(Nigeria)
Level - First paragraphs