YAMMATA BIYU MA SU ABIN MAMAKI
Ahmad Lasmar Ibrahim
Bashir Isah Muhammad

Wadansu 'yammata guda biyu suna cikin tafiya, sai suka iso kofar gidan sarki. Sai suka nemi guri suka zauna domin su huta. Sai babbar ta ce, ina ma a ce sarkin garin nan ya yarda ya aure ni.

1

Sai in haifa masa 'yan tagwaye. Daya da cibiyar azurfa daya da ta zinare.

2

Sai dayar kuma ta ce, "in da a ce sarkin garin nan ya sanni, sai ya bani kwaryar shinkafa guda daya in dafa masa. Duk garin nan birni da kauye sai kowa ya ci ya koshi."

3

Ashe wani mutum yana labe yana jin su, sai ya tafi ya gaya wa sarki. Koda sarki ya ji haka sai ya sa a je a taho da su. Sannan ya umarce su su maimaita abin da suka fada. Koda suka maimaita sai sarki ya amince.

4

Sai sarki ya ba da lefe a ka daura musu aure da babbar.

5

Ita kuma dayar a ka ba ta kwaryar shinkafa guda daya ta dafa. Birni da kauye a ka ci a ka koshi.

6

Bayan wata tara da daura aure, sai babbar kuwa ta haifi 'yan tagwaye guda biyu. Guda da cibiyar azurfa dayan da cibiyar zinare.

7

Sai uwar ta tafi bayan gida domin ta yi wanka. Daga nan sai kishiyarta ta kwashe yaran ta watsa su ta kan katanga cikin tafasa. Sannan ta debo kadangaru guda biyu ta saka a madadin jaririran.

8

Koda sarki ya zo ya ce mai aka samu? Sai a ka ce masa 'ya'yan kadangaru. Sai ran sarki ya baci.

9

Sai sarki ya ce mata " 'yar uwarki ta cika alkawari amma ke ba ki cika naki ba."

10

Daga nan sai ya ce ta koma bayan gidan kusa da masai ta zauna ita da abin da ta haifa.

11

Tana nan a wajen tare da beraye har ta dauki cuta. Daga nan ta mutu. Sarki kuma bai sake auren mata irin su ba.

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
YAMMATA BIYU MA SU ABIN MAMAKI
Author - Ahmad Lasmar Ibrahim
Illustration - Bashir Isah Muhammad
Language - Hausa(Nigeria)
Level - First paragraphs