LABARIN KURWA DA ZAKI
Abida Yahuza Yusuf
Mujtaba Ali Badawi

A wani gari an yi wani sarki azzalumi.

1

Saboda zalincinsa idan mutum ya yi masa laifi, sai ya saka shi cikin wani daki tare da zaki domin zakin ya cinye shi.

2

Wata rana sai Kurwa ya yi tafiya tare da matarsa, a kan hanyarsu sai suka biyo ta cikin wani daji.

3

Sai suka ci karo da wani zaki ya taka itace mai tsini, yana kwance yana nishi yana zubar da hawaye.

4

Sai Kurwa ya je kusa da zakin yana shafa shi.

5

Har zakin ya fahimci ba cutar da shi zai yi ba.
Sai Kurwa ya debo wasu ganyayyaki ya dandaka.

6

Ya kama kafar zakin ya shafa masa a wajen ciwon. Sannan ya samu wani kyalle ya kulle masa ciwon. Suka cigaba da tafiya da matarsa. Suka bar zakin a wajen.

7

Ana nan sai wata rana mafarauta suka farauto zakin nan suka kaiwa sarki.

8

Sai wata rana Kurwa ya yiwa sarki laifi. Sai sarki ya sa a ka kama shi a ka kai shi dakin da ya tsare zakin nan domin ya cinye shi. Koda zaki ya ga Kurwa sai ya gane, ya dinga kada jela yana kewaya Kurwa cikin farinciki.

9

Shi ma Kurwa ya gane zakin. Sai ya dinga shafa shi. Sarki da mutane suka yi mamakin me ya sa zaki ya ki cinye Kurwa? Sai sarki ya tambayi Kurwa domin ya sanar da shi labarinsa.

10

Sai Kurwa ya kwashe labarinsa ya sanar da sarki. Sai sarki ya yi masa afuwa. Daga nan sai Kurwa ya zama abokin zakin nan suke yawo tare.

11

Sai sarki ya yi alkawarin ya daina zalinci. Kuma zai dinga yi wa mutane afuwa. Tunda dabba ma ta san alheri bare kuma dan'adam. Sai mutanen gari suka yi murna da hakan.

12
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
LABARIN KURWA DA ZAKI
Author - Abida Yahuza Yusuf
Illustration - Mujtaba Ali Badawi
Language - Hausa(Nigeria)
Level - First paragraphs