Maryam yar Makaranta
Asmau Lawan Ayuba
Salma Balarabe Yusuf

A wani gari mai suna Gwarzo. Akwai wata yarinya mai suna Maryam.

1

Ba ta san karatu sai dai wasa kawai da gudun makaranta.

2

Su kuma kawayenta suna son karatu suna fada mata gaskiya.

3

Sai wata rana a ka yi jarrabawa ta zangon karatu na karshe.

4

Sai Maryam ba ta ci jarrabawar ba. Ta zo ta karshen aji.

5

Sai a ka yi canjen aji ban da ita.

6

Sai ta ji haushi sosai. Ta yi kuka mai yawa, saboda ta zo ta karshen aji.

7

Sai a ka kara yin jarrabawa a zangon karatu na farkon ajin da take maimaitawa.

8

Sai ta dage da karatu, ta yi bita sosai kafin jarrabawa.

9

Bayan da sakamakon jarrabawa ya fito, Maryam ta ci jarrabawarta duka. Ta zo ta biyar, ta yi murna sosai.

10
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Maryam yar Makaranta
Author - Asmau Lawan Ayuba
Illustration - Salma Balarabe Yusuf
Language - Hausa(Nigeria)
Level - First paragraphs