

A wani babban gari me suna Rici, akwai wani ƙauye mai suna Gimi, 'yan ƙauyen sun kasance sunfi ba wa talla muhimmanci,
a ƙauyen akwai wani mutum mai suna malam Musa. Ya kasance ma aikacin gwamnati. malam Musa ya tsaya tsayin daka ganin 'yar sa magajiya tayi karatun zamani.
Bayan shekarun aikinsa na gwamnati sun cika, sai ya koma sana'ar noma. A wata shekara, noman malam Musa bai yi kyau ba, har ya kasance sun rasa abun da zasu ci. 'Yan ƙauyen sukayi ta surutu cewa yakamata ya bar 'yarsa ta fara talla.
Duk sanda magajiya zata tafi makaranta, sai yara su dinga mata dariya. Tun tana kuka har tazo ya daina damun ta.
A kwana a tashi, magajiya ta kammala makarantar gaba da firamare. Rana daya mai shela ya zo sanarwa, cewa: "mai gari yana gayyatar duk wanda ya kammala karatun sakandare, gwamnati za ta ba shi gurbin karatu ƙasar waje".
Magajiya ta samu gurbin karatu a kasar waje amma bata so rabuwa da 'yan uwanta ba musamman iyayenta. Baban ta malam Musa yayi mata nasiha sosai a kan ta dage sossai a karatunta sannan ta zama mai gaskiya da rikon amana.
bayan ta fara karatu sai ta kasance mai kwazo ta fannin likitanci, saboda kwazo, gaskiyar ta da kuma rikon amanar ta aka ba ta aiki ta zama babbar likita
a kowane lokaci tana tuna i me zai kawo ci gaba a qauyen su kamar bunkasa ilimin 'ya'ya mata
bayan wasu shekaru magajiya ta dawo daga kasar waje da arziki mai yawa,nyan qauyen su sukayi nadamar maganganun da sukayi a baya game da ilimin ya mace
iyayen magajiya sun farin cikin ganin yadda yarsu ta zama abar kwantance a qauyen gaba daya. A karshe magajiya ta yi nasarar bude makaranta a qauyen su domin bunkasa ilimin ya mace.

