Wata rana wani manomi ya dawo daga gona a gajiye, sai ya tambayi matarsa a bashi abincinsa, sai akace masa babu.
1
Sai ransa ya baci, ya yanke shawarar sakinta. da kawunsa yaji labari sai ya kirashi yayi masa nasiha kada ya soma kodan ya'yansu.
2
Washe gari kawun sa yaje gidan ya yiwa matar nasiha akan idan mijinta ya dawo ta bashi hakuri.
3
tafiyar sa keda wuya se Manomin nan ya dawo, matarsa tai masa maraba sannan ta bashi hakuri a bisa abin da ya faru. tace masa ta gane kuskurenta
4
Yana fara'a yace haba komai ya wuce na yafe miki, ya ciro wasu yan kudi yace ga wannan ayi cefane harda dan tantakwashi ki watsa mana a miya suka bushe da dariya bakidaya.
5
Ya fita yana daga mata hannu. yace, "sai na dawo"
6
Ta tura aka yi mata cefane ta dafa musu abinci mai dadi, ta zubawa mijinta a kwanon sa ta boye sannan ta zubawa yara ma sukaci suka koshi
7
rayuwarsu ta koma dai-dai babu korafi babu barazana. Hakuri maganin zaman duniya.
8
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Hakuri Maganin zaman duniya
Author - Zahra'u Bala Illustration - Muhammad Garba Wudil, Isaac Okwir, Adonay Gebru, Rob Owen Language - Hausa (Nigeria) Level - First paragraphs