Rayuwarmu
Hassana Suleiman
Kenneth Boyowa Okitikpi

BABI NA ƊAYA.
"Wayyo Allah!" Muryar mahaifiyata na jiyo cikin kuka, hakan ya sa ni farkawa daga dogon tunanin da na afka. A razane na nufo tsakar gida, ina faman haɗa hanya saboda rashin ƙwarin jiki. Ina fitowa na ganta yashe a ƙasa.

1

rungume da ƙanina Manu cikin jini, kamar an yanka wata babbar dabba. Ban san lokacin da na zuɓe ƙasa dirshan ba. Ji na yi gaba ɗaya duniyar tana juyawa, saboda tsananin tashin hankali.
"Sun kashe min ɗana…"

2
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Rayuwarmu
Author - Hassana Suleiman
Illustration - Kenneth Boyowa Okitikpi
Language - 0
Level - First paragraphs