

Musa yaro ne mai ƙoƙari, sai dai fitinanne ne. Yana zaune da mahaifanshi a ƙauyen kagadama.
Musa yaro ne mai zaluntar yara 'yan uwanshi. Wani lokaci ma har dabbobi ma in ya gani ko a gida ko hanya sai ya basu wahala.
Rannan akan hanyar sa ta dawowa daga makaranta, sai ya tsinto kyanwa. Yana ganin ta sai ya sa hannu ya ɗauke ta, ya kai ta gidan su.
Baban shi yace, kai musa? Ka mayar da kyanwar nan inda ka ɗauko ta, ka daina bata wahala.
Musa bai ji maganar baban shi ba sai ya kulle kyanwar a akurki bai bata abinci.
Wata rana yana kwance a ɗaki da daddare, sai ya ga kyanwar nan ta zama ƙatuwa, ta nufo shi da bakin ta a buɗe, hakoranta zako-zako za ta haɗiye shi.
Ta fara daga kafafun sa, suka shige cikin bakin ta gaba ɗaya, sai musa ya farka daga bacci ashe Mafarki yake!
Gari na waye wa, musa ya mayar da ita inda ya ɗauko ta, daga nan yayi alƙawarin gyara halayen sa.

