Sanin Damisar Bunu
Abubakar Saidu-Sado
Philip Hayab John

A wani gari mai suna Magarya. Anyi wani mutum mai suna Bunu.

1

A garin Magarya, a kan zauna a yi ta hira da bada labarai masu ƙayatarwa

2

Da aka zo kan Bunu sai ya ce nasa labarin a kan damisa ne

3

Bunu ya gyara murya, ya fara cewa "Damisa kamar kyanwa ta ke".

4

Sai kowa ya ce "Lallai, haka ne".

5

Ya ce kuma "Tana da tsawon bindi".

6

Sai aka ce “Ummm, gaskiyar ka!

7

Lokacin da Bunu ya fahimci ya fara birge jama'a.

8

Sai ya yi farat ya ce "Ai lokacin da muke yara, malamin mu ya taɓa nuna mana damisa a bakin rafi."

9

Damisa, tana da ƙahon ta biyu masu tsawo kamar na barewa."

10

Sai kowa ya ƙyalƙyace da dariya ana yi masa ba'a.

11

"Ta tabbata Bunu baka san damisa ba!" Suna faɗi suna dariya.

12

Bunu ya ji takaici sosai.

13

Daga lokacin sai ya ce "Daga yau ba zan
sake ba da labarin abinda ban sani ba.

14
You are free to download, copy, translate or adapt this story and use the illustrations as long as you attribute in the following way:
Sanin Damisar Bunu
Author - Abubakar Saidu-Sado, Lawali Kaura, Philip Hayab John, Sani Masama Garba, Timothy Anche
Illustration - Philip Hayab John
Language - Hausa (Nigeria)
Level - Longer paragraphs